Matsalar tsaro: Miyagun yan bindiga sun ƙone fadar basaraken gargajiya a Najeriya

Matsalar tsaro: Miyagun yan bindiga sun ƙone fadar basaraken gargajiya a Najeriya

  • Wasu yan bindiga da ba'a gano ko su waye ba sun kona fadar wani basarake a jihar Imo
  • Rahotanni sun bayyana cewa shi kanshi basaraken da iyalansa da kyar suka sha, yayin da suka tsere caji ofis na yan sanda
  • Wannan na zuwa ne kwana ɗaya kacal bayan arangamar da aka yi tsakanin sojoji da matasan yankin

Imo - Wasu tsagerun yan bindiga da ba'a gane ko suwaye ba sun ƙone fadar Dagacin Etekwuru dake ƙaramar hukumar Ohaji/Egbema, jihar Imo.

Punch ta rahoto cewa maharan sun ƙone motarsa highlander jeep da wasu dukiyoyinsa yayin harin.

Lamarin wanda ya faru ranar Alhamis da daddare, ya zo ne awanni 24 bayan arangama tsakanin matasa da sojoji a yankin.

Jihar Imo
Miyagun yan bindiga sun kone fadar basaraken gargajiya a Najeriya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rikicin ya yi sanadiyyar hallaka soja guda daya, yayin da jami'an sojin suka ɗauki fansa, ta hanyar ƙone wasu gidaje a ƙauyen Agrarian.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda tsagerun suka ƙone fadar Dagacin

A ranar Alhamis da daddare, maharan sun mamaye gidan Dagacin, yayin da suka duba basu gan shi ba ko ɗaya daga cikin iyalansa, sai suka cinnawa gidan wuta da motocinsa.

Dagacin ya shaidawa manema labarai cewa ya gudu ne zuwa hedkwatar yan sanda dake Mmahu domin tseratar da rayuwarsa.

A cewarsa shi da matarsa suna cikin gidan lokacin da miyagun suka farmake su, kuma sun tsira da rayuwarsu ne ta hanyar badda kama.

Shin maharan sun kashe wani?

Dailytrust ta ruwaito Basaraken yace:

"Da misalin ƙarfe 10:30 na dare ranar Alhamis wasu tsageru suka shigo gidana, suka farfara gilasai da kofofi suƙa ƙona gidan."
"Sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi, hakan yasa na kasa tserewa da ni da matata da kuma ɗa na. Daga nan na fara kiran a kawo mun ɗauki daga yan sanda, amma ba su zo ba har sai da lamarin ya yi ƙamari."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Har Cikin Gida Sun Kashe Basarake da Wasu 2 a Jihar Arewa

"Yan sanda sun iso wajen ƙarfe 11:45 amma ba su haɗu da yan bindigan ba, ina zargin waɗannan yaran ne da suka kashe soja."

A wani labarin kuma Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa yan fashin daji sun fara sako mutanen da suka kama saboda babu abincin ba su.

Dakta Abdullahi Shinkafi, mataimakin kwamitin tsaro, yace matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka suna haifar da ɗa mai ido.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262