Gwamna Ganduje zai bude sabuwar jami'a a wannan kwalejin ilimin a jihar Kano

Gwamna Ganduje zai bude sabuwar jami'a a wannan kwalejin ilimin a jihar Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta amince ta ɗaga liƙafar kwalejin ilimi ta Sa'adatu rimi zuwa matakin jami'a
  • Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shine ya bayyana haka yayin da ya karɓi bakuncin shugabannin kwalejin
  • A cewar Ganduje, gwamnatinsa da shi karan kansa zai yi alfahari ace kwalejin tana bada shaidar kammala karatun digiri

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da kiran da ake masa na ɗaga matsayin kwalejin Sa'adatu Rimi zuwa jami'a.

Freedom Radio ta ruwaito cewa kwalejin ta jima tana miƙa ƙoƙon bararta ga gwamna Ganduje kan ya maida ita matsayin jami'a.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da kwamitin gudanarwa na kwalejin Sa'adatu Rimi suka kai masa ziyara gidan gwamnati.

Gwamna Ganduje na jihar Kano
Gwamna Ganduje zai bude sabuwar jami'a a wannan kwalejin ilimin a jihar Kano Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

Dakta Ganduje yace zai bada goyon baya ɗari bisa ɗari wajen ɗaga matsayin makarantar zuwa matakin jami'a.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Jihar Kano: Gwamna Ganduje Ya Yi Tsokaci Kan Matakin da Suke Dauka da Tsagin Malam Shekarau

Zamu yi alfahari idan Sa'adatu Rimi ta zama jami'a - Ganduje

Hakazalika yace zai tuntuɓi hukumar kula da jami'o'i ta ƙasa (NUC) kan lamarin, a jawabinsa, yce:

"A ko da yaushe fatana da kirana shine a inganta ɓangaren koyo da koyarwa, zan yi alfahari sosai idan aka ce yau Sa'adatu Rimi ta zama makarantar dake bada ilimin digiri."
"Bana tsammanin aikin maida kwalejin matsayin jami'a zai kawo tsaiko, saboda ba za'a kashe wasu kuɗaɗe ba, kowane kayan aiki akwaisu a makarantar."

Me ya kai shugabannin kwaleji wurin Ganduje?

Shugaban kwalejin Sa'adatu Rimi, Farfesa Yahaya Isa Bunkure, shine ya jagoranci tawagar makarantar zuwa wurin gwamna Ganduje.

Tawagar makarantar ta je da nufin sanar da gwamnan cikar kwalejin shekara 40 da kafuwa, da kuma sake neman a ɗaga matsayinta zuwa jami'a.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta dakatar da gangamin taronta a wannan jihar

A wani labarin na daban kuma Yan sanda sun fara bincike kan yadda jami'an tsaro suka kaɗa kuri'a a zaben APC na tsagin Ganduje

Wasu hotunan bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda wani ƙaramin sufetan yan sanda ya kaɗa kuri'a a zaɓen APC na Kano.

Mataimakin sufetan yan sandan ƙasar nan mai kula da shiyya ta ɗaya, Abubakar Sani Bello, ya bada umarnin bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262