Rikici ya barke bayan sojoji sun bindige 'yan kungiyar awaren IPOB har 5
- Rikici ya barke a wani yankin jihar Abia yayin da wasu 'yan IPOB suka fito yawon gangami
- Duk da cewa rahotanni ne da ba a tabbatar dasu ba, amma an ce sojoji sun karbe 'yan IPOB biyar
- An ce sun fito ne da suka ji labarin an kawo shugaban kungiyarsu ta IPOB kotu a babban birnin tarayya
Abia - Jaridar Daily Sun ta rahoto cewa, an samu tashin hankali a Arochukwu ta jihar Abia a ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba yayin da jami'an tsaro ke fafatawa da 'yan kungiyar awaren IPOB a yankin.
Wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba ya nuna cewa mutane hudu da ake zargi 'yan kungiyar IPOB ne ana fargabar an kashe su a yayin fafatawar.
Duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da abin da ya jawo harbe-harben ba, wata majiya ta yankin ta ce nan take da yankin ya samu labarin kawo shugaban IPOB Nnamdi Kanu kotu a Abuja don fuskantar shari'a, wasu mambobin IPOB sun hau kan tituna.
Majiyar ta ce 'yan kungiyar ta IPOB sun nuna farin ciki cewa Kanu yana raye, sabanin rahotannin da suke samu game da lafiyar shugaban na 'yan aware.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma lokacin da suka isa wani bankin First Bank na garin, 'yan IPOB sun fuskanci sojoji.
Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun ce yayin da sojojin ke ji da 'yan kungiyar IPOB da ke cikin jerin gwanon, sai rikici ya faru sannan aka bindige 'yan kungiyar biyar.
An ce wannan ya haddasa barkewar rikici a Arochukwu, yayin da mazauna garin suka yi ta tserewa don neman tsira, inda tuni suka tsere cikin daji, in ji rahoton Daily Trust.
Nnamdi Kanu ya musanta zargin da ake masa a gaban kotu
A bangaren Kanu kuwa, The Cable ta ruwaito cewa, an sake gurfanar da Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar ‘yan asalin yankin Biyafara (IPOB) a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin ta’addanci.
Kwanan nan gwamnatin tarayya ta sake shigar da laifukan da ake tuhumarsa da shi guda bakwai kari a kan laifuka biyar da a baya yake amsa su, wadanda suka hada da aikata cin amanar kasa da ta’addanci.
An fara zaman kotun a ranar Alhamis da karfe 10 na safe.
Asali: Legit.ng