Fastoci sun kwantar da mambobinsu suka riƙa zagbarsu da bulala a coci don gwaji, bidiyon ya janyo cece-kuce

Fastoci sun kwantar da mambobinsu suka riƙa zagbarsu da bulala a coci don gwaji, bidiyon ya janyo cece-kuce

  • Wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna wani fasto yana yi wa mambobin cociinsa bulala a kan mimbari
  • Faston ya rika yi wa mata da maza bulala a mazaunansu don gwada ko ko sun shirya zama 'yan cocinsa, Legit.ng ta tattaro
  • Wasu yan Nigeria sun soki faston kan abin da suka bata wa addini suna, yayin wasu suka ga laifin mambobin da suka yarda ake musu bulala

Mutane da dama masu amfani da shafukan sada zumunta sun nuna bacin ransu da mamaki bayan bullar wani bidiyo da ke nuna fastoci suna yi wa mambobinsu bulala a coci.

Kamar yadda ya ke a bidiyon Instagram da @nikkys_world1 ta wallafa, mambobin cocin maza da mata sun kwanta a kasa yayin da fasto ke lafta musu bulala.

Read also

Yadda mawallafin ShaharaReporters ya sha duka a hannun 'yan daba a harabar kotun Abuja

Bidiyon fasto yana yi wa mabiyansa bulala da 'belt' a coci don yi musu gwaji ya janyo cece-kuce
Fasto yana yi wa mabiyansa bulala da 'belt' a coci don yi musu gwaji Hoto: @nikkys_world1
Source: Instagram

Masu rera wakokin coci sun rika sakin sauti a yayin da fasto ke tsulawa mambobinsa belt a mazauninsu yayin da suka kwanta a kasa a kan mimbari.

Mambobin cocin da bisa alamu na biyaya ga fastonsu ba su ce uffan ba a yayin da ya ke binsu daya bayan daya yana musu bulala.

Legit.ng ta tattaro cewa fastocin na yi wa mambobinsu bulalan ne domin su gwada su idan har da gaske sun shirya zama mambobin cocin.

Martanin da wasu 'yan Nigeria suka yi game da lamarin

@jarazirozay8 ya ce:

"Wannan fa kamar kungiyar asiri ne, ba ka wanda ya ke murza belt ba yayin da ya murtuke fuska?"

@yekinihalimataa shi kuma cewa ya yi:

"Kamar sun yi musu laifi ne a baya, shi yasa suke hukunta su."

Read also

Bidiyo da hotunan maciji mafi girma da aka taba gani a duniya

@ada_francis_oonwuka ta bayyana ra'ayinta kamar haka:

"Wannan zai rika jibgan mabiyansa a duk lokacin da ya ga dama da sunan addini."

@super_gift26 ta rubuta:

"Da masu dukan da wadanda ake duka duk suna da manyan matsaloli a tattare da su, muna kokawa da yadda yan sanda ke cin zali, amma gashi fastoci na cin zali."

@gabbyebube ya ce:

"Ni dai ban san dalilin da zai sa wani ya amince da irin wannan cin mutuncin da rainin wayyo ba kawai don yana son zama mamban coci? Abin ya fi karfin hankali na."

Source: Legit

Online view pixel