Bidiyon yadda ma'aurata suka sayo gida daga wani gari suka kawo shi garinsu
- Wasu ma'aurata 'yan kasar Kanada sun bar duniya da jin mamaki yayin da suka kurar da gidansu gaba daya daga wani tsibiri
- Daniele Penney da Kirk Lovell sun gamu da tsadar gidaje a Arewacin Amurka saboda haka suka yanke shawarar siyan gida daga wani wuri
- Ma'auratan sun zabi sayen gidan mai shekara 100, yayin da suke tattaunawa da tsoffin masu gidan Daniele ya ce yana da "kyau"
Wasu ma'aurata 'yan kasar Kanada sun shahara a duniya bayan da suka kaurar da gidansu a wani sashe na teku.
A cewar rahotanni daban-daban na kafofin watsa labarai, bayan saye ma'auratan sun yanke shawarar kaurar da kyakkyawan gidan nasu zuwa wani wuri daban.
Ma'auratan da aka bayyana da Daniele Penney da Kirk Lovell, sun san cewa samun gida a Arewacin Amurka zai bukaci kudi masu yawa. Don haka suka yanke shawarar tumbuke dukkan gidan tare da ketarawa dashi a saman ruwa.
Business Insider ya ce Penney da Lovell sun so su sayi gida a Newfoundland a garin McIvers amma da suka ji wasu ma'aurata suna shirin ruguza gidan mai shekaru 100, sai suka yanke shawarar sanin farashin gidan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta yaya suka dauki gidan bayan sayensa?
An ba da rahoton cewa ma'auratan sun yanke shawarar ciniki da masu gidan don kulla yarjejeniya mai kyau, kuma suka yarda.
Penney ta yi bayanin matakin kuma ta ce gidan yana da kira na musamman a ciki wanda shi ya sa suka yanke shawarar tafiya dashi.
A bangare guda, News Chant ta ba da rahoton cewa Lovell ya ce yana son ganin ko gidan zai iya tafiya a saman ruwa.
An nakalto Lovell yana cewa wannan wani abu ne da aka yi a shekarun 1960 kuma babu wata fasaha a lokacin.
A cikin bidiyon da ke yawo a dandamali daban-daban, ana iya ganin gidan yana kewaye da jiragen ruwa wadanda suka taimaka wajen tabbatar da cewa ba a samu matsala ba.
Dama ta samu: Yadda kamfani zai biya ku N13.5m kawai don ku kwanta a kan gado
A wani labarin, Baya ga rage damuwa da taimakawa jiki, kwanciya akan gado yana rage gajiya amma a yanzu ya zama damar aiki mai tsoka kamar yadda wani kamfani ke son biyan mutane kudi su kwanta.
Ladbible ta ba da rahoton cewa wani kamfani mai kera gadon alatu da kawa da aka fi sani da Crafted Beds yana karbar cike-ciken mutane don gwajin wata katifa.
Aikin zai ba masu sha'awa £24,000 (N13,589,203.20) a kowace shekara wanda idan aka kasafta shine £2,000 (N1,132,433.60) kowane wata.
Asali: Legit.ng