Gwamnan Arewa ya ce shigowa da fulani ke yi daga kasashen waje ya janyo rashin tsaro

Gwamnan Arewa ya ce shigowa da fulani ke yi daga kasashen waje ya janyo rashin tsaro

  • Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya ce shigowar Fulani daga kasashen ketare ne ya ke kawo rashin tsaro a Najeriya
  • Ya bayyana hakan ne a Makurdi, babban birnin jihar yayin da shugabannin gargajiya daga jihar Nasarawa su ka kai ma sa ziyara
  • Kamar yadda takardar da babban sakataren yada labaran gwamnan ta bayyana, sarkin Keffi ne ya jagoranci shugabannin

Binuwai - Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai ya ce afkawar Fulani daga kasashen waje zuwa garuruwa ne ya ke janyo rashin tsaro a fadin kasar nan.

The Cable ta ruwaito cewa Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Makurdi, babban birnin jihar bayan ya amshi ziyarar wakilan shugabannin gargajiya daga jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

‘Yan Najeriya na fama da yunwa, talauci da rashin tsaro – Sheikh Dahiru Bauchi ya koka

Gwamnan Arewa ya ce shigowa da fulani ke yi daga kasashen waje ya janyo rashin tsaro
Gwamna Ortom na Jihar Benue. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Kamar yadda takardar wacce Nathaniel Ikyur, babban sakataren yada labaran gwamnan, ya ce sarkin Keffi, Shehu Chindo ne ya jagoranci wakilan.

Shugabannin gargajiyan sun kai wa gwamnatin jihar Binuwai ziyara ne don jaje akan balaguron farauta da Elias Ikoyi Obekpa, shugaban kasar Idoma ya yi.

Yayin amsar su, Ortom ya ce kabilun Tibi, Fulani da sauran ‘yan Najeriya sun zauna tare cikin zaman lafiya kafin Fulani daga kasar waje su fara shigowa Najeriya ba tare da an duba su ba.

Ya ce shigowar Fulanin ba tare da an bincike su ba ne ya janyo matsalolin tsaro

A cewar sa shigar su cikin kasa ba tare da an bincike su ba shi ne sanadin matsalolin tsaron da kasar nan ta ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa

Dangane da killataccen kiwo, Ortom ya yi bayani, inda ya ce dokar za ta taimaka wa makiyaya saboda za ta hana kiwo a budadden wuri da satar shanu.

Gwamnan ya kara da yaba wa kokarin gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, sakamakon kokarin samar da zaman lafiya tsakanin jihohin 2.

Ya kara da bayyana cewa shugabannin gargajiya ne su ke da alhakin samar da zaman lafiya tsakanin al’umma.

A bangaren su, Chindo ya gabatar da wata takarda daga gwamnan jihar Nasarawa zuwa ga Ortom inda ya ce ya ji labarin mummunan lamarin da ya auku da Och’Idoma.

The Cable ta ruwaito yadda mummunan lamarin ya shafi jihar Binuwai, Nasarawa da gabadaya Najeriya.

Ya kara da cewa duk ma su samun kudi daga rikicin manoma da makiyaya sai sun yi danasani.

Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri

A wani rahoton, Mai garin Lokoja, Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi III, ya dakatar da yin duk wani sha’ani da dare a cikin garin Lokoja da duk wasu anguwanni da su ke da makwabtaka da Lokoja har sai yadda hali ya yi.

Kara karanta wannan

Sakin Nnamdi Kanu zai kawo ƙarshen rashin tsaro a kudu maso gabas, Sanata Ubah

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayar da umarnin nan ne sakamakon yadda ya ga bata gari su na amfani da damar shagulgulan dare wurin cutar da jama’a a cikin babban birnin jihar.

Kungiyoyin asiri su kan yi amfani da damar bukukuwan dare da sauran sha’anoni a Lokoja da kewaye wurin kai wa jama’a farmaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: