Muhyi: Kotu ta bukaci ganin kakakin majalisar jihar Kano da wasu mutane 5
- Babbar kotun tarayya da ke zama a Kano ta bukaci ganin kakakin majalisar jihar a ranar Laraba da wasu mutane 5
- Hakan ya biyo bayan korafin da shugaban hukumar korafin jama’a da yaki da rashawa da aka dakatar, Muhyi Rimin-Gado ya shigar a kan su
- Sauran wadanda ake karar sun hada da antoni janar na jihar, babban akawun jihar, kwamishinan ‘yan sanda da kuma sifeta janar na ‘yan sanda
Jihar Kano - Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta bukaci kakakin majalisar jihar da sauran mutane 5 su bayyana a gaban ta kamar yadda ta zo a ruwayar Daily Nigerian.
Umarnin ya biyo bayan korafin da shugaban hukumar korafin jama’a da yaki da rashawa wanda aka dakatar na jihar Kano, Muhyi Rimin-Gado ya shigar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sauran wadanda ya ke karar sun hada da Antoni janar na jihar Kano, babban akawun jihar, kwamishinan ‘yan sanda na jihar da kuma sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Alkalin kotun, Justice Jane Iyang, wanda ya bayar da umarnin ya bukaci su bayyana a gaban kotun cikin kwana 5 kuma kada kotun ta amince da wata bukatar su.
Iyang ya ce ana bukatar ganin duk wadanda ake karar cikin kwana 5 kuma ya dage karar zuwa ranar 3 ga watan Nuwamba don sauraro.
Rimin-Gado ya bukaci kotu ta dakatar da wadanda yake kara daga bincike akan sa
Dama wanda ya shigar da karar, Rimin-Gado ta lauyan sa, Muhammad Dan’azumi, ya bukaci kotu ta dakatar da mutane 6 da ya ke karar daga bincike akan sa da kuma kama shi.
Karar ta yi daidai da umarni na 2 doka ta 1 yanki na 34, 35, 36, 37, 41 da 42 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 2009, da kuma doka ta 26 (b) doka ta 7.
Dan’azumi ya bukaci kotun ta duba lamarin inda ya kara da cewa wadanda ya ke kara sun saba wa dokar da babbar kotun jihar Kano ta bayar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
NAN ta ruwaito yadda alkalin babbar kotun jihar Kano, Justice Sanusi Ado-Ma’aji a ranar 23 ga watan Yuli ya dakatar da babban akawun jihar Kano da sauran mutane 2 daga ci gaba da bincike akan Rimin-Gado.
NAN ta ruwaito yadda aka dakatar da shi daga majalisar jihar Kano a ranar 5 ga watan Yuli tun daga ofishin babban akawun jihar.
Asali: Legit.ng