Likitoci sun samu nasarar dasawa dan Adam kodar Alade a Amurka

Likitoci sun samu nasarar dasawa dan Adam kodar Alade a Amurka

  • Da alamun sauki ya samu kan matsalar lalacewar koda da mutane ke fama da shi
  • Masu bincike a Amurka na ganin za'a iya wa mutum dashin kodar alade
  • An gwada wannan jikin wata mata kuma an samu sakamako mai gamsarwa

Amurka - Karon farko, an samu nasarar dasa kodar Alade cikin dan Adam ba tare da wata matsala ba, wani sabon bincike da ka taimakawa mutane masu matsalar cutar koda.

Reuters ta ruwaito cewa an gudanar da wannan aiki ne a jami'ar New York dake kasar Amurka.

An yi amfani da kwayar hallitar Aladen da aka canza ne bayan cire wani kwaya wanda zai iya kawo matsala jikin mutum, binciken ya nuna.

An gwada wannan bincike ne kan mara lafiyar da kwakwalwarta ta mutu kuma take fama da ciwon koda bayan amincewar iyalansa, masu binciken suka bayyanawa Reuters.

Kara karanta wannan

Karon farko, an samu nasarar yiwa dan Adam dashin zuciyar Alade a Amurka

Tsawon kwanaki uku, an dasa sabon kodar cikin jininta amma ba'a dinke ba domin ganin yadda abun zai gudana.

Gwaje-gwajen da aka yi kan sabon kodar ya nuna cewa babu wata matsala, Masanin aikin tiyata wanda ya jagoranci aiki, Dr Robert Montgomery, ya bayyana.

Yace:

"Kodar ta samar da adadin fitsarin da ake bukata tamkar kodar mutum."

Likitoci sun samu nasarar dasawa dan Adam kodar Alade a Amurka
Likitoci sun samu nasarar dasawa dan Adam kodar Alade a Amurka Hoto: Reuters
Asali: UGC

Ya kara da cewa babu hujjar cewa akwai wata matsala kamar da yadda aka fuskanta lokacin da aka dasa kwayar cutar da ba'a sauya ba cikin wasu dabbobi.

Bugu da kari, matsalar karancin creantinine - wani alama dake nuna matsalar koda - ya dawo daidai bayan dashin, Dr Robert Montgomery ya kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng