Da Dumi-Dumi: An damke wani ɗauke da makami a cikin masu zanga-zangar tunawa da EndSARS
- Jami'an yan sanda sun damke wani matashi ɗauke da makami a cikin masu zanga-zanga a Tollgate jihar Legas
- A ranar 20 ga watan Oktoba, 2020, matasa suka gudanar da zanga-zangar ƙin jinin SARS, Shekara ɗaya kenan yau
- A halin yanzun yan sanda na cigaba da amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa mutane a wurin
Lagos - Jami'an tsaro sun cafke ɗaya daga cikin masu zanga-zangar tunawa da EndSARS ɗauke da adda a Tollgate, jihar Legas, kamar yadda dailytrust ta rahoto.
Daruruwan matasa dake zanga-zangar tunawa da EndSARS bayan shekara ɗaya cif, sun tattaru a Tollgate, ranar Laraba, duk da gargaɗin da rundunar yan sanda ta yi.
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ba zata bar masu zanga-zangan su haɗu a wurin ba, domin gudun kada yan ta'adda sun mamaye su.
Sai dai hukumar yan sanda ta amince motoci da sauran abin hawa su cigaba da zirga-zirgan su a yankin wurin, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Shin an amince matasa su tuna da EndSARS?
Kwamishinan yan sanda na jihar Legas, Hakeem Odumosu, yace hukumomi sun amince matasan su yi zanga-zangar su daga ƙarfe 8:00 zuwa 10:00 na safe.
Amma matasan sun ƙeƙashe ƙasa, sun cigaba da tattaruwa a Tollgate, ɗauke da allunan rubutu kuma suna rera waƙar sukar gwamnati.
Jami'an yan sanda sun harba wa masu zanga-zangan hayaƙi mai sa hawaye, nan take suka watse amma cikin ƙanƙanin lokaci suka sake tattaruwa.
Yadda aka kama mai ɗauke da makami
Bayan wani ɗan lokaci, wani matashi sanye da ɗamammen wando da riga mai kala-kala, ya shiga komar yan sanda ɗauke da adda.
Yayin da yan sanda suka kama shi, sauran masu zanga-zanga suka fara neman a sake shi.
Tun farko dai, jami'an sun kame wasu daga cikin yan zanga-zangar, har da ɗan jarida, amma daga baya kwamishinan yan sanda ya bada umarnin a saki ɗan jaridan.
Shin an samu masu ɗauke da bindigu?
CP Odumosu, yace:
"Na tattauna da su, sun tabbatar mun zasu kammala zanga-zangarsu ƙarfe 10:00 na safe, saboda haka duk waɗanda suka cigaba yanzun ba su da hankali."
"Wasu daga cikinsu na ɗauke da bindiga, wasu da wukake, wasu da guduma, shin su kuma yan zanga-zanga ne ko yan daba?"
A wani labarin kuma Gwamnatin tarayyar Najeriya tace ko mutum ɗaya sojoji ba su kashe ba a wurin zanga-zangar EndSARS shekarar data wuce
Ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed, yace babu wata shaida ko da ta gawar mutum ɗaya ne, da aka kawo wa gwamnati.
A cewar ministan an kashe sojoji shida da yan sanda sama da 30 a lokacin zanga-zangan amma sam bai dami kowa ba.
Asali: Legit.ng