'Yan sandan Kano sun cafke masu kai wa 'yan bindiga man fetur har Katsina
- 'Yan sandan jihar Kano sun yi ram da wasu mutum biyu dauke da jarkoki 5 na man fetur a Kano
- Katsinawan mazauna karamar hukumar Jibiya sun siya fetur din domin siyarwa 'yan bindigan Katsina
- An tsare motocin J5 guda 2 inda aka gan su dauke da kayan abinci amma sun boye jarkokin fetur a cikin buhunan sikari
Kano - Rundunar 'yan sandan jihar Kano sun cafke wasu mutum biyu da ake zargin suna samarwa da 'yan bindigan jihar Katsina man fetur daga Kano.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, DSP Abdullahi Haruna-Kiyawa, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Talata a Kano, Daily Nigerian ta wallafa.
Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da Musbahu Rabi'u mai shekaru 31 da kuma Jamilu Abdullahi mai shekaru 37, dukkansu mazauna karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.
Haruna Kiyawa ya ce an kama wadanda ake zargin ne a wasu motoci kirar J5 dauke da jarkokin man fetur wadanda suka boye a cikin buhunan sikari.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"A ranar 15 ga watan Oktoba wurin karfe 12 da rabi na rana, wata kungiyar 'yan sanda da suka samu jagorancin Abubakar Hamma yayin sintiri a Fagge, sun tsare wasu motocin J5 da aka dankarawa kayan abinci.
"Bayan an tsare su tare da dubawa, an samu jarkoki biyu masu lita 25 dauke da man fetur wadanda aka boye a buhunan sikari," yace.
Ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun sanar da cewa "sun zo Kano ne daga Katsina kuma sun siya man fetur a jarkoki wadanda za su kai Jibiya domin siyarwa 'yan bindiga da tsada".
Wadanda ake zargin sun bayyana cewa, "wannan ne karo na biyu da aka kama mu yayin da muke kokarin safarar man fetur."
Haruna Kiyawa ya yi bayanin cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Samaila Shuaibu-Dikko, ya bada umarnin tsananta bincike kan lamarin wanda ya kara da cewa za a kai su kotu.
Kwamishinan 'yan sandan jihar ya yi kira ga mazauna jihar da su zama masu sa ido a muhallinsu tare da kai rahoton duk wani abu da suka yi zargi ga 'yan sanda, Daily Nigerian ta wallafa.
Ya yi kira ga masu gidajen mai a jihar da su kiyaye siyarwa da mutanen da basu sani ba fetur mai yawa a cikin jarka.
Dalla-dalla: Yadda 'yan bindiga suka yi wa jama'a kisan kiyashi a kasuwar Sokoto
A wani labari na daban, kisan kiyashin da 'yan bindiga suka yi wa jama'a a kasuwar Goronyo da ke gabashin jihar Sokoto a daren Lahadi ya tada hankula.
Ganau sun sanar da Daily Trust a ranar Litinin cewa, mummunan farmakin da aka kai ya kunshi 'yan ta'adda daga mabanbantan kungiyoyi.
Sun ce miyagun sun ajiye banbancinsu tare da hada kai inda suka tsinkayi kasuwar mako-mako ta Goronyo suka dinga harbe-harbe.
Asali: Legit.ng