Allah gwanin kyauta a lokacin da ya so: Wata mata mai shekaru 70 ta haifi danta na fari
- Wata mata mai shekaru 70 a duniya ta haifi danta na fari a kasar Indiya
- An tattaro cewa matar ta kasance daya daga cikin uwayen da suka samu haihuwarsu ta farko a shekarun tsufa a duniya
- Sun samu haihuwar ne da taimakon likitoci ta hanyar IVF
Allah ya azurta wata tsohuwa da haihuwar danta na fari a lokacin da take da shekaru 70 a duniya, a kasar Indiya.
An tattaro cewa matar mai suna Jivunben Rabari ta kasance daya daga cikin uwayen da suka samu haihuwarsu ta farko a shekarun tsufa a duniya.
Shi kuma mijin nata mai suna Maldhari yana da shekaru 75 ne a duniya a lokacin da suka samu haihuwarsu ta farko, inda suka sami ‘da namiji.
Sun nuna wa manema labarai yaron da Allah ya azurta su da shi yayin da suka ce sun haife shi ne ta hanyar IVF.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rabari ta bayyana cewa bata da wani katin shaida don tabbatar da shekarunta, amma ta fada ma manema labarai cewa shekarunta 70 a duniya.
Hakazalika, wata mata ‘yar Indiya, mai suna Erramatti Mangayamma, ta haifi ‘yan biyu mata a shekarar 2019, tana da shekaru 74 a duniya.
Rabari da Malhari wadanda suka fito daga wani karamin kauye mai suna Mora a Gujurat, kasar Indiya,sun shafe tsawon shekaru 45 da aure kuma suna ta kokarin neman haihuwa amma Allah bai basu ba.
Sun yi nasarar samun haihuwa ta hanyar IVF, bayan sun manyanta sosai. Likitan ma’auratan Naresh Bhanushali ya ce wannan lamari nasu yana daga cikin ‘yan tsiraru da ya taba gani.
Dr Bhanushali ya ce: 'Lokacin da suka fara zuwa wurinmu, mun fada musu cewa ba za su iya haihuwa ba a irin wannan shekaru na tsufa, amma suka dage.
Ya ce:
"Sun ce da yawa daga cikin dangin su ma sun yi hakan. Wannan na daya daga cikin yan kadan da na taba gani."
Shafin Linda Ikeji ne ya wallafa hotunan ma'auratan da dansu a Instagram.
Aure da aurar da kananan yara yana halaka 'ya'ya mata 60 a kowanne rana, Bincike
A wani labarin kuma, kungiyar Save the Children International ta ce auren wuri yana halaka fiye da yara mata 60 a ko wacce rana, kungiyar ta tallafa wa yara mata ta duniya ta bayyana hakan a ranar yara mata ta duniya.
Bisa kiyasi, ana aurar da 44% na yara matan Najeriya kafin su cika shekaru 18, wanda Najeriya tana daya daga cikin kasashen da su ka fi yin auren wuri a duk fadin duniya kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Kamar yadda Kunle Olawoyin, manajan sadarwa na Save the Children ya bayyana, ya ce dakyar a rage yawan auren wuri a Najeriya sakamakon tsaka mai wuya da mata suke rayuwa a ciki a halin yanzu.
Asali: Legit.ng