Hotunan tukunyar da aka kirkira domin girka abinci biyu a lokaci daya, jama’a sun yi martani

Hotunan tukunyar da aka kirkira domin girka abinci biyu a lokaci daya, jama’a sun yi martani

  • Wani dan Najeriya ya ja hankalin jama’a a shafukan soshiyal midiya bayan bayyanar hotunan wata tukunya da ya kera
  • Tukunyar na dauke da sashi biyu ta yadda mutum zai iya girka abinci iri biyu a lokaci guda
  • Mutane da dama sun yaba da hakan duba da yadda iskar gas na girki yayi tsada

Wani mutumi ya haddasa cece-kuce a kafofin sada zumunta bayan hotunan wata tukunya da ya kera sun yi fice a yanar gizo.

An kera tukunyar ne gida biyu ta yadda mutum zai iya dafa abinci iri biyu a lokaci guda domin saukaka rayuwa musamman a yanzu da ake tsadar abubuwan girki.

Hotunan tukunyar da aka kirkira domin girka abinci biyu a lokaci daya, jama’a sun yi martani
Hotunan tukunyar da aka kirkira domin girka abinci biyu a lokaci daya, jama’a sun yi martani Hoto: 24hrsreport
Source: UGC

‘Yan Najeriya da dama sun yaba da kirkirar wannan tukunya da mutumin yayi inda suka bayyana hakan a matsayin ‘tunani mai kyau’ duba ga tsadar iskar gas na girki a yanzu.

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Duk da cewa jama’a da dama sun yaba da wannan ra'ayin, wasu na ganin hakan ba wani sabon abu bane.

A kan samu irin wadannan tukwane da zai ba mutum damar dafa abinci da dama a lokaci guda.

Ga hotunan tukunyar da mutumin da ya kerata kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa a Instagram:

Ga martanin ‘yan Najeriya kan tukunyar:

sommy_of_fash ya yi martani:

“Wannan ya yi kyaushinkafa da miya a hade ”

handel_benny ya ce:

“Wannan tsantsar baiwa ce. Allah ya albarkaci fasaharsa.”

chy_baybeh ta ce:

“Allah ya yiwa wannan mutumin albarka, saboda gas yayi tsada.”

Gas din girki ya fi karfin talakawa: 'Yan Benue sun rungumi aiki da icce da gawayi

A wani labari na daban, mun kawo cewa mazauna garin Makurdi, sun yanke shawarar komawa ga aiki da icce da gawayi yayin da farashin iskar gas ke kara hauhawa.

Kara karanta wannan

Yajin-aiki: Sai Majalisa ta kawo dokar hana yaran mala’u yin Digiri a Jami’o’in waje - ASUU

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a gidan mai na Bolek a Makurdi, ana cika tukunyar gas na 12.5kg kan N8500 sabanin N4500 da ake siyarwa a farkon shekarar.

Wata mazauniyar garin, Jummai Kande, wacce ta kasance a gidan man don cika tukunyar 5kg, ta ce ta biya N4000 sabanin N1400 da take biya wajen siyar adadin a farkon shekarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng