An tsinci sassan jinjiri da aka yi gunduwa-gunduwa da shi a Kano
- Mutanen gari sun gano sassan jikin jinjiri a cikin itace da sunkoro a Wudil a jihar Kano
- Mai unguwar Sakau, Mallam Muhammadu Sule, ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Lahadi
- An kai sassan jikin asibitin Wudil inda likitoci suka tabbatar anyi gunduwa-gunduwa da jinjirin ne
Jihar Kano - An tsinci sassan jikin wani jinjiri da aka datsa gunduwa-gunduwa a unguwar Sakau a garin Wudil na jihar Kano a ruwayar Daily Trust.
Mazauna Sakau a Sabon Gari da ke Wudil sun ce sun farka a safiyar Lahadi sun tsinci sassan jikin jinjiri, yana mai cewa an tsinci kafufuwa da kai a wurare daban-daban cikin sunkoro.
Mai unguwar Sakau, Mallam Muhammadu Sule, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce sun sanar da hukumomin tsaro da yan sanda domin a gudanar da bincike.
A cewarsa:
"Wani da ake kira Manaja ne ya sanar da ni cewa an tsinci kafar jinjiri cikin itace a safiyar ranar Lahadi. Na isa wurin na gani amma na ga 'yan sanda sun iso. Nan take na sanar da dagaci, shi kuma ya ce in sanar da yan sanda da yan Hisbah.
"Mun yi bincike amma bamu gano sauran sassan jikin jinjirin ba. Sai bayan mun birne kafar, kimanin awa biyu aka sanar da ni an gano kan jinjirin cikin sunkoro. Mun sake sanar da yan sanda, sai da muka sake hako kafar da muke birne."
Muhammad ya kuma ce an kai kafafuwa a kan jinjirin zuwa asibitin Wudil domin likitoci su yi gwaji inda suka tabbatar an datse jikin jinjirin ne gunduwa-gunduwa.
Shehu Abdullahi, wanda ganau ne kan lamarin, ya shaidawa Daily Trust cewa suna zargi ne cewa wata ne ta haifi jinjiri, ta yi gunduwa-guduwa don jinjirin don tsafi.
Dagacin kauyen Sabon Garin Wudil, Alhaji Garba Me Disai, wanda shima ya tabbatar da lamarin ya yi kira ga mutane su rika sa ido kan abubuwan da ke faruwa su kuma sanar da jami'an tsaro.
Basarake a Arewa ya haramta bukukuwa cikin dare a ƙasarsa saboda harkokin ƙungiyoyin asiri
A wani rahoton, Mai garin Lokoja, Alhaji Mohammed Kabiru Maikarfi III, ya dakatar da yin duk wani sha’ani da dare a cikin garin Lokoja da duk wasu anguwanni da su ke da makwabtaka da Lokoja har sai yadda hali ya yi.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya bayar da umarnin nan ne sakamakon yadda ya ga bata gari su na amfani da damar shagulgulan dare wurin cutar da jama’a a cikin babban birnin jihar.
Kungiyoyin asiri su kan yi amfani da damar bukukuwan dare da sauran sha’anoni a Lokoja da kewaye wurin kai wa jama’a farmaki.
Asali: Legit.ng