Kaduna: Jami'an tsaro sun halaka 'yan bindiga 10 a Giwa, sun ceci mutum 1
- Jami'an tsaro na hadin guiwa a jihar Kaduna sun ragargaji 'yan bindiga a Kwanan Bataru da ke Fatika a karamar hukumar Giwa
- A take jami'an tsaron suka halaka 'yan bindiga 10, suna raunata wasu miyagun tare da kone wata bukkarsu
- A wannan halin ne jami'an tsaron suka ceci wani mutum daya wanda miyagun suka sato suke jiran kudin fansa
Giwa, Kaduna - 'Yan bindiga goma da ke tafka barna a cikin jihar Kaduna sun hadu da ajalinsu bayan arangamarsu da jami'an tsaro, Aruwan ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Jami'an tsaron hadin guiwa sun tattaru inda suka yi arangama da 'yan ta'addan a Kwanan Bataru da ke wajen garin Fatika ta karamar hukumar Giwa kuma suka yi artabu.
"A yayin musayar wutan, goma daga cikin 'yan bindigan sun sheka lahira yayin da wasu suka tsere da raunikan harbin bindiga.
"Yan bindigan da suka sha da kyar sun bar babura masu tarin yawa, bindiga daya, wayar salula, tocila da wasu layu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Daya daga cikin bukkokin da 'yan bindigan ke amfani da su wurin tsare wadanda suka yi garkuwa da su an banka mata wuta," Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida ya ce a wata takarda.
Wani Alhaji Abubakar Usman, wanda akwai yuwuwar an sato shi ne daga jiha makusanciya, an cece shi.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya jinjina wa jami'an tsaron kan yadda suka yi fito na fito da 'yan ta'addan. Gwamnan ya na yi wa jami'an tsaron fatan nasara a kokarin da suke yi a jihar.
Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda
A wani labari na daban, a kalla rayuka 12 aka kashe yayin farmakin da 'yan bindigan daji suka kai kauyen Sakajiki da ke masarautar Kauran Namoda a jihar Zamfara.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a ranar Juma'a.
Ya ce an samu wadanda suka rasa rayukansu yayin aukuwar lamarin kuma ba don taimakon jami'an tsaro ba, da abun ya fi haka muni.
Asali: Legit.ng