Labarin Abubakar: Matashin Bakano, matukin jirgin sama da ya koma sana'ar dinki

Labarin Abubakar: Matashin Bakano, matukin jirgin sama da ya koma sana'ar dinki

  • Ishaq Ibrahim Abubakar matashin bakano ne da ya koma sana'ar dinki duk da samun horarwa kuma ya zama matukin jirgi
  • Abubakar ya bayyana cewa, akwai wani fanni daya tak da ya dace ya kware domin zama matukin jirgin haya a duniya
  • Sakamakon rashin wannan damar ne Abubakar ya koma dinki domin rufawa kansa asiri tare da koyarwa da ya ke yi

Kano - Ishaq Ibrahim Abubakar matashi ne mai shekaru 38 a duniya kuma ya na daga cikin matasa 100 da gwamnatin Kano ta dauka nauyin horarwarsu domin zama matukan jirgin sama a kasar ketare a 2013.

Sai dai, duk da kammala horarwar cike da nasara kuma ya dawo gida, dole ta sa ya koma sana'ar dinki domin rufawa kai asiri.

Kara karanta wannan

Jigawa: An kama makiyayi da shanunsa 73 da awaki 14 saboda kutse cikin gona

Daily Trust ta ruwaito cewa, an haifa Abubakar a kwatas din Fagge da ke karamar hukumar Fagge ta jihar Kano. Ya yi dukkan karatunsa a jihar har zuwa matakin digirin farko a jami'ar Bayero da ke Kano.

Labarin Abubakar: Matashin Bakano, matukin jirgin sama da ya koma sana'ar dinki
Labarin Abubakar: Matashin Bakano, matukin jirgin sama da ya koma sana'ar dinki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Cike da hazaka Abubakar ya samu lasisin tukin jirgin 'yan kasuwa da daraja ta farko bayan kammala karatunsa a Jordan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma kuma tun bayan dawowarsa Najeriya a 2015, bai samu damar tuka jirgi ba. Ya cigaba da zama babu aikin yi duk da ya na da shaidar karatuttuka a Multi-Crew Course (MCC) certificate da Crew Resource Management Certificate (CRM) da jarabawar RELTER.

Wannan halin da Abubakar ya shiga ya na da alaka ne da wasu bukatu wadanda suka shafi makuden kudi da za a kashe kafin a dauke shi aikin fara tukin jirgin sama.

Abubakar ya ce: "Bukata ce a kowanne sashi na duniya cewa bayan an kammala karatun tukin jirgi, akwai wata horarwa da za a yi domin kwarewa.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ga FG: Makuden kudi kafintoci da direbobi ke samu, a wajabta musu haraji

"Lasisin matukin jirgin sama kadai bai isa ya sa matukin ya samu aiki da jiragen haya ba har sai ya samu kwarewa a fanni daya tak, wanda hakan kuwa zai dogara ne da zabinsa ko na kamfanin."

A don haka, dole ta sa Abubakar ya koma dinki wanda sana'a ce da ya koya tun lokacin da ya ke tasowa. Wannan sana'a kuwa ta na taimaka masa wurin rufin asiri hadi da koyarwar da ya ke yi, Daily Trust ta wallafa.

Kwankwaso ya magantu kan titsiye shi da hukumar EFCC ta yi

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta labaran da ke yawo a kafafen yada labarai kan cewa hukumar yaki da rashawa, EFCC, ta yi ram da shi.

Tsohon gwamnan ya tabbatar da cewa, da kan shi ya kai wa hukumar ziyara har ofishinsu domin wanke sunansa kan wani korafi da aka kai gaban ta a kan shi, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Matawalle ya rantsar da shugabannin gudunarwa a kananan hukumomi 14

Kwankwaso, tsohon ministan tsaro, ya kwatanta korafin da zugar 'yan siyasa tare da zargin cewa 'yan siyasan da ke son ganin sun tozarta shi ne suka kai korafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: