Goron Juma'a: Auren Jari Hujja, Tare da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.
A wannan karo, Malam ya yi bayani kan lalata dake faruwa tsakanin matasa na auren jari hujja.
Da yawa daga cikin maza da mata suna makara wajan yin aure da wuri saboda wasu dalilai, neman wajan hutu, da kyakyawa, doguwa mai hanci fara, shi kuma duk bashi da abinda yake faɗa.
Wadannan abubuwa suna cikin abin da ke kawo jinkirin aure. Mafiya faruwa daga cikinsu a ɓangaren maza akwai son aurar mace mai kyau wacce take kala.
Da yawa maza zaka samu mazan da masu kuɗi ko matsayi na ilmi da mulki ba ,suna ɗorawa kansu cewa sai mace fara , doguwa , mai kaza da kaza suke so su aura. Irin siffofin da shi kansa bai da su , kuma masu irin wannan siffar ba zasu so shi ba , matsawar ba wani matsayi ko dukiya yake da ita ba.
Akan samu wasu mazan kaɗan dake kallafawa kansu auren ƴaƴan mawadata ko masu matsayi don su ma shiga babban gida a ci daula da su a sama.
Ko kuma su dinga lissafin cewa a gaba za su samu farar gawa. Ko kuma a ƙalla za a dinga taimaka masa da wani abu. Wannan yakan kawowa irin waɗannan mutane jinkirin aure da rashin daraja da ƙima a idon mutane da surukai musamman idan suka fahimci ka auri ƴarsu ne don abin dake hannunsu.
Banda wannan, irin waɗannan mazajen ba samun ƙarfin hali da cikakken iko da faɗa a ji a gidajensu, daga matan da ƴaƴansu.
Ba kasafai matansu suke musu biyayya ba. Ƙarshe sai a wayi gari mutum ya zama sakarai , mijin ta ce sai abin da matar take so za a yi , dai dai ne ko kuskure ne.
A musulunce ba laifi ba ne mutum ya auri mace saboda kuɗinta amma fa ba manufa ce mafi inganci da ɗorewa ba.
Sannan musulunci ya baiwa maza dama su auri irin matar suke so , kamar yadda ya baiwa mata dama su zaɓi irin namijin da suke so.
Wannan matsalar tana kawo mazaje da yawa jinkirin aure da matsala bayan aure kamar yadda ya gabata.
ABUBUWAN DAKE KAWO WA MATA JINKIRIN AURE TA ƁANGAREN MATA.
Sannan a ɓangaren mata za ka ga wasu sun sa buri wajen irin mijin da take so wanda wannan ma ya kan kawo jinkirin a daɗe ba a yi aure ba.
Wasu mata saboda wata ƙawarta ko ‘yar’uwarta ta auri wani hamshakin mutum ko mai kuɗi ko mai ilimi ko mai mulki.
Sun ga yadda aka yi hidima aka kashe maƙudan kuɗaɗe, to sai su dinga jiran su ma sai sun sami irin wannan ya fito ya aure su , domin su ma a yi musu irin wannan hidima.
Ba su san cewa al’amura a hannun Allah suke ba. Tana iya yiwuwa ta auri talakan ya juye ya koma mai kuɗin. Ko ta auri mai kuɗin ya juye ya koma talaka. Ko ta auri mara darajar ya koma mai daraja.
An sha ganin mutanen da ba kowa ba amma Allah ya ɗaukaka su ya mayar da su wani abu. Kuma mun sha ganin waɗanda suke jin su wani abu ne amma sai Allah ya sauke su.
To ka ga ashe kenan burin auren irin mijin wata ba ma’auni ba ne in za a yi aure. Kuskure ne a ce lallai sai wanda ya samu wata ɗaukaka ta duniya za a aura - domin ita ɗaukaka ta kufcewa kuma ana iya samun ɗaukakar daga baya.
Kawai abin da ake so tarbiya da kuma zuciya da kuma hali na gari. Wannan shi a ke buƙata a miji in za a aure shi haka matar ma.
Wasu matan ma irin wannan burin yakan kai su ta tarewa a gidan ƴar uwarta dake auren wani mai matsayi wai kawai don masu matsayin abokansa su ganta su aure ta.
A ƙarshe idan akai rashin sa a sai wasu su yi amfani da kwaɗayinta su lalata mata rayuwa kuma ba su aure ta.
Samu da rashi duk na Allah ne. Kuma Bahaushe yana cewa ita duniya rawar ƴan mata ce. Wani lokacin na gaba sai dawo baya.
Asali: Legit.ng