Gwamnati Ta Shiga Tsakani, Ta Sa an Kamo Ango da Iyayen Amarya bayan Daura Aure

Gwamnati Ta Shiga Tsakani, Ta Sa an Kamo Ango da Iyayen Amarya bayan Daura Aure

  • Ango, iyayen ango da amarya sun shiga hannun hukuma bayan yi wa yarinya 'yar shekara 13 auren dole a jihar Enugu
  • Ma'aikatar harkokin mata da yara ta Enugu ta ce an yi wa yarinyar aure ba tare da amincewarta ba kuma gata karama
  • Kwamishinar mata ta ce an mika wadanda aka kama har da matar da ta hada auren ga jami'an tsaro domin ci gaba da bincike

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Enugu, Nigeria - Gwamnatin jihar Enugu ta bayyana bacin ranta kan yadda wasu iyaye suka yi wa yarinya 'yar shekara 13 auren dole.

Bisa haka, gwamnati ta kama ango da iyayensa da kuma iyayen amaryar gaba daya, da wata mata mai suna, Mrs Patience, wacce ake zargin ita ta hada auren.

Jihar Enugu.
Taswirar jihar Enugu Hoto: Legit.ng
Source: Original

Dalilin kama ango da iyayen amarya

Kara karanta wannan

Fitaccen jarumin fim a Najeriya ya bayyana ana tsaka da jita jitar ya mutu

The Nation ta ce an kama su ya biyo bayan kin amsa gayyata daga Ma’aikatar Harkokin Mata da Yara bayan bidiyon auren ya karade shafukan sada zumunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoto ya nuna cewa an daura auren karamar yarinyar ba tare da amincewarta ba kuma ba ma ta san komai game da aure ba a kauyen Amufie, karamar hukumar Igbo-Eze ta Arewa a Enugu.

Kwamishinar ma’aikatar mata ta Enugu, Hon. Ngozi Eni, ta ce an gano cewa yarinyar, wadda aka bayyana da Amarachi, yar shekaru 13 kacal, an daura mata aure bisa tilas ba tare da amincewarta ba.

Eni ta ce:

“Mun gayyace su su zo su bayyana dalilin aurar da ƙaramar yarinyar amma suka ƙi zuwa. Wannan ya nuna ba su da gaskiya, shi ya sa muka kama su.”

Dokar Enugu ta haramta auren yara

Kwamishinar ta kara da cewa dillaliyar da ta hada auren ba ta san komai ba game da dokar da ta haramta auren ƙananan yara, in ji Daily Post.

Yanzu haka yarinyar tana karkashin kariya ta gwamnatin jihar Enugu kuma ta shaida wa jami’ai cewa auren dole aka mata, sannan an hana ta zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

Ngige: Ministan Buhari ya fadawa Obi yadda 'yan ta'adda suka bude masa wuta

Uwar ango ta yi ƙoƙarin kare lamarin da hujjar cewa danta shi kaɗai ne amma ta yi shiru bayan an tunatar da ita cewa dokar jihar Enugu ta haramta auren kananan yara.

Gwamna Peter Mbah.
Gwamna Peter Mbah a fadar gwamnatin jihar Enugu Hoto: Peter Ndubuisi Mbah
Source: Facebook

Bayan fadawa ango, iyayen ango, da iyayen amarya laifin da suka aikata a doka, ma'aikatar mata ta mika su ga jami'an tsaro domin karisa bincike.

Kwamishinar mata, Eni ta ce za a soke auren gaba ɗaya kuma gwamnati za ta taimaki Amarachi ta gyara rayuwarsa, kuma za ta mida ita makaranta.

An fasa hada 'yan TikTok aure a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Hisbah ta soke shirin auren da aka tsara tsakanin shahararrun 'yannTikTok , Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya da Basira Yar Guda Daya.

Wannan mataki dai na zuwa ne duk da umarnin da wata kotun majistare ta bayar a baya cewa a shirya musu aure cikin kwanaki 60.

Bayan bincike da tattaunawa da bangarorin biyu, hukumar Hisbah ta gano cewa sun yi kokarin amfani da batun auren ne domin kaucewa hukunci kan zargin badala.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262