Tarihi da Muhimman Abubuwa game da Marigayi Shugaba Buhari

Tarihi da Muhimman Abubuwa game da Marigayi Shugaba Buhari

  • Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rasu yau Lahadi, 13 ga Yuli, 2025 a wani asibiti a birnin London
  • Buhari ya jagoranci Najeriya a matsayin shugaban soja (1983–1985) da kuma shugaban kasa na dimokuradiyya (2015–2023)
  • Bincike ya nuna cewa an fi sanin Muhammadu Buhari da tsattsauran ra'ayi kan yaki da cin hanci da kuma kishin kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Najeriya ta rasa ɗaya daga cikin manyan ‘yan siyasa da shugabanninta na tarihi, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu yau Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a wani asibiti a London.

Fadar shugaban kasa ta tabbatar da rasuwar, inda ta bayyana cewa za a shirya dawowar gawarsa zuwa Najeriya domin birne shi.

Buhari a zauren majalisar dinkin duniya
Buhari a zauren majalisar dinkin duniya. Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa da fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta game da tarihi da rayuwar Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Rasuwar Buhari: Tinubu ya tura Shettima ya ɗauko gawar tsohon shugaban kasa a London

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari da ya taba mulkin soja daga 1983 zuwa 1985, sannan kuma ya sake mulkin dimokuradiyya daga 2015 zuwa 2023, ya kasance daya daga cikin shahararrun shugabannin Najeriya.

An yi masa lakabi da gwarzon yaki da cin hanci da rashawa tare da kasancewa mutum mai tsananin gaskiya da rikon amana.

Farkon rayuwar Buhari da karatun da ya yi

An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga Disamba, 1942 a garin Daura, jihar Katsina. Mahaifinsa Adamu, ya rasu ne yana ƙarami, hakan ya sa mahaifiyarsa Zulaiha ce ta raine shi.

Ya fara karatunsa a Daura daga 1948 zuwa 1952, sannan ya halarci makarantar sakandaren Katsina (Government College, Katsina) daga 1956 zuwa 1961.

Rayuwar Buhari a aikin soja da mulkin soja

Buhari ya shiga rundunar sojan Najeriya a 1961, inda ya samu horo a Kaduna, daga baya kuma ya je kasashe kamar Ingila, India da Amurka.

Ya rike mukamai da dama kamar Gwamnan Arewa maso Gabas, kwamandan runduna, da Ministan Albarkatun Man Fetur.

Kara karanta wannan

'An yi babban rashi': Tsohon shugaban kasa Buhari ya rasu, ƴan Najeriya sun magantu

Muhammadu Buhari ya jagoranci Majalisar Soji kafin ya karbi mulki a juyin mulkin 1983, inda ya zama shugaban kasa na soja har zuwa 1985.

Yin ritayar Buhari da aikin da ya yi da PTF

A lokacin mulkin Janar Sani Abacha, an nada Buhari a matsayin shugaban Hukumar Tallafin Man Fetur (PTF) a 1994.

A karkashinsa, hukumar ta aiwatar da ayyuka a fannonin hanya, ilimi, ruwa, lafiya da abinci. An yaba masa kan yadda ya gudanar da hukumar ba tare da cin hanci ba.

Shigar Buhari siyasa da takara sau uku

Buhari ya shiga siyasa a 2003 a karkashin ANPP, inda ya sha kaye sau uku a hannun Olusegun Obasanjo (2003), Umaru Musa Yar’adua (2007) da Goodluck Jonathan (2011).

Duk da haka, Buhari bai gajiya ba wajen fafutukar siyasa da niyyar ceto Najeriya daga matsalolin da suka dabaibayeta.

Tarihin nasarar Buhari a zaben 2015

Punch ta wallafa cewa a shekarar 2013, jam’iyyun adawa na ACN, CPC, ANPP da wasu na PDP suka hade suka kafa jam'iyyar APC.

A karkashin wannan jam’iyya, Buhari ya yi nasara a zaben 2015, ya kayar da shugaba mai ci Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Shugaba Muhammadu Buhari ya rasu a London

Buhari tare da Bola Tinubu
Buhari tare da Bola Tinubu. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Twitter

An rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2015. Ya kara samun nasara a 2019, inda ya kammala wa’adinsa a 2023.

Iyalan Buhari da wasu abubuwan tarihi

Buhari ya yi aure da Safinatu Yusuf daga 1971 zuwa 1988. Daga baya ya auri Aisha Halilu a 1989. Ya bar yara da dama bayan rasuwarsa.

A lokacin rayuwarsa, Buhari ya fi son rayuwa mai sauki da tsari, kuma an fi saninsa da rashin sha'awar dukiya da tarin kayan duniya.

Za a dauko gawar Buhari a London

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta sanar da rasuwar shugaba Muhammadu Buhari a yau.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta yi babban rashi bayan mutuwar Buhari.

Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya tafi London dauko gawar Buhari Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng