Obasanjo Ya Fadi Abin da Ya Aikata Abacha Ya Tura Shi Kurkuku
- Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda rashin iya yin shiru kan batutuwan ƙasa da na duniya ya kai shi gidan yari
- Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa matsalar da ta ke damun Najeriya ta sa shi neman shugabancin ƙasa a shekarar 1999
- Shugaba Obasanjo ya yabawa taron matasan Afirka da ƙungiyar Future Africa Leaders Foundation ta shiryaa 2013 a Ogun
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa rashin iya yin shiru kan muhimman batutuwan ƙasa da na duniya ya janyo aka kai shi kurkuku.
Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa an kai shi kurkune a ƙarƙashin mulkin soja a lokacin marigayi Janar Sani Abacha a shekarar 1995.
Daily Trust ta wallafa cewa Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da shugabannin matasa masu tasowa daga sassan Afirka da aka yi a Abeokuta, Jihar Ogun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da mai taimaka masa a fannin yada labarai, Kehinde Akinyemi ya fitar, Obasanjo ya bayyana cewa matsalar Najeriya ta sa ya nemi shugabanci a 1999 domin ceto ƙasar.
Abacha: Dalilin kai Obasanjo kurkuku
Olusegun Obasanjo ya tuna yadda ya shiga gidan yari sakamakon yin sharhi kan batutuwan ƙasa da na duniya ba tare da tsoro ba.
Obasanjo ya ce,
“Na shiga soja, kuma ina shekaru 42 na kammala aikina a matsayin sojan ƙasa. Bayan haka, na fara aikin noma, amma a wannan lokaci aka tura ni gidan yari, wanda ba abin da na so ba ne.
“Rashin yin shiru kan al’amura ya sa na shiga gidan yari. Duk abin da na ga ya kamata a yi sharhi a kai, na yi.
"Bayan na fito daga gidan yari, na tarar da Najeriya tana cikin mawuyacin hali da ya sa mutane ke ganin dole ne a ceci ƙasa.”
Ra’ayin Obasanjo kan basussukan Afirka
A yayin tattaunawar, Obasanjo ya nuna damuwa kan yadda kasashen Afirka ke ɗaukar basussuka da suka bayyana a matsayin sakaci da cin hanci.
“Yawancin basussukan ba za a iya bayyana yadda aka kashe su ba. Wasu kuwa saboda cin hanci ne kawai aka karbo su.”
- Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya yabawa matasan Afrika
Olusegun Obasanjo ya yaba wa shugabannin matasan Afirka da suka halarci taron da ƙungiyar Future Africa Leaders Foundation ta shirya a jihar Ogun.
Channels Television ta wallafa cewa tsohon shugaban kasar ya yaba wa Fasto Chris Oyakhilome, wanda ya kafa tafiyar matasan tun shekarar 2013.
Obasanjo ya ce;
“Abin da Fasto Chris Oyakhilome yake yi tun 2013 abin alfahari ne. Ko da wasu na ganin shirin ba zai amfani jama'a sosai ba,
"Amma duk da karancinsa, zai fa'idantar da jama'a. Na gamsu da wannan shiri kuma ina yi masa fatan alheri.”
Taron ya ƙunshi tattaunawa kan matsalolin Afirka da mafita, inda Obasanjo ya yi kira ga matasan da su kasance masu kishin ƙasa da hangen nesa wajen jagorantar al’umma.
'Yar'adua ya soke yarjejeniyar Obasanjo
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana abin da ya faru kan matatun man Najeriya a baya.
Olusegun Obasanjo ya ce ya kulla yarjejeniya da Aliko Dangote kan matatun amma marigayi Umaru Musa Yar'adua ya soke ta.
Asali: Legit.ng