Yadda Aiki Ya Hana Gwamnan Jigawa Halartar Jana'izar Mahaifiyarsa

Yadda Aiki Ya Hana Gwamnan Jigawa Halartar Jana'izar Mahaifiyarsa

  • A yau Laraba aka yi sallar jana'izar mahaifiyar Gwamna Umar Namadi a garin Kafin Hausa na jihar Jigawa
  • Marigayiya Hajiya Maryam Namadi ta rasu tana da shekaru kusan 90 kuma manyan mutane sun halarci jana'izar
  • Bayan gano cewa gwamna Namadi bai samu halartar jana'izar ba, Legit ta yi bincike a kan dalilin rashin zuwansa sallar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - A yammacin Laraba, 25 ga Disamba, 2024, aka gudanar da sallar jana'izar mahaifiyar Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi a garin Kafin Hausa.

Marigayiya Hajiya Maryam Namadi ta rasu da safiyar wannan rana bayan gajerar jinya, tana da shekaru kusan 90.

Namadi
An yi jana'izar mahaifiyar gwamnan Jigawa. Hoto: Garba Muhammad
Asali: Facebook

Hadimin gwamna Umar Namadi, Garba Muhammad ya wallafa yadda jana'izar ta gudana a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Mahaifiyar gwamnan Jigawa ta rasu, ya nemi addu'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Namadi bai halarci jana'izar ba?

Legit ta gano cewa a yanzu haka gwamna Umar Namadi na kan hanyar dawowa daga ƙasar China bayan ziyarar aiki ta kwanaki biyar da ya tafi.

Wannan shi ne babban dalilin rashin halartar gwamna Umar Namadi jana'izar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam da aka gudanar a Kafin Hausa.

Mataimakin Gwamnan Jihar, Aminu Usman Gumel, da sauran manyan jami’an gwamnatin jihar sun tarbi bakin da suka zo ta'aziyya

Manyan baki da su ka halarci sallar jana'izar

Sallar jana'izar ta samu halartar manyan baki da suka fito daga ciki da wajen jihar, ciki har da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf; Sanata Barrister Ibrahim Hassan Hadejia.

Shugaban Majalisar Sarakunan Jigawa, Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar ya halarci jana'izar.

Sauran sun hada da Sanata Danladi Sankara, Sanata Abdulaziz Usman Turabu, da shugabannin hukumomi da sauransu.

Jigawa ta yi jarjejeniyar noma da China

Kara karanta wannan

Yaki da yunwa: Gwamna ya gayyato 'yan China domin koyar da noman zamani

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta kulla yarjejeniya da wani kamfanin kasar China domin bunkasa noma da hakaba tattalin arziki.

Mai girma gwamna Umar Namadi ne ya jagoranci kulla yarjejeniyar da kansa kuma ya ce za a horas da monama yadda za su yi aiki da fasahar zamani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng