Bwala: An Titsiye Mai Sukan Muslim Muslim da Ya Shiga Gwamnatin Tinubu
- Tsohon hadimin Atiku Abubakar da ya shiga gwamnatin Bola Tinubu ya yi hira da yan jarida bayan shugaban kasa ya ba shi muƙami
- Daniel Bwala ya shahara da sukan tikitin Muslim Muslim a kafafen sadarwa a lokacin yakin neman zaben shekarar 2023
- Bwala ya bayyana cewa tun a watan Janairu ya dawo goyon bayan shugaba Bola Tinubu kuma zai cigaba da tafiya tare da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An titsiye mai sukan Muslim Muslim da ya shiga gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bayan karɓar mukamin Bola Tinubu, Daniel Bwala ya dawo kare gwamnatin da ya rika sukar takararta baya.
YM Yusuf ya wallafa bidiyon hirar da Channels Television ta yi da Daniel Bwala bayan karɓar mukami a gwamnatin Tinubu a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An titsiye mai sukan Muslim Muslim
An tambayi Daniel Bwala dalilin karɓar matsayi a gwamnati duk da cewa har yanzu Tinubu da Kashim Shettima ba su canza addini ba kuma ya shahara da sukan Muslim Muslim a baya.
Daniel Bwala ya ce ba zai amsa tambayar ba saboda ya riga ya amsa ta a watan Janairu kuma ba shi da lokacin da zai bata a kanta.
Da aka matsa masa lamba sai Daniel Bwala ya ce ko sau 100 za a maimaita tambayar ba zai amsa ta ba.
Managar cire tallafin man fetur
The Nation ta wallafa cewa Daniel Bwala ya ce shugaban kasa ya yi kokari wajen cire tallafin man fetur a Najeriya.
Bwala ya ce gwamnatocin baya sun nufi cire tallafin amma suka gaza, kuma a yanzu haka an fara ganin amfanin tsare tsaren Bola Tinubu.
Shirin Daniel Bwala da Kashim Shettima
Bayan karɓar matsayi, Sanata Ali Ndume ya bukaci Bwala ya ba Kashim Shettima hakuri saboda sukansa da ya yi a kan Muslim Muslim a baya.
Sai dai Daniel Bwala ya ce tun a farko ya yi magana da Kashim Shettima har ma sun yi wasa da dariya.
Tinubu ya yi martani ga Obasanjo
A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi martani ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan sukar Bola Ahmed Tinubu da ya yi.
Hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu a harkokin sadarwa, Sunday Dare ne ya ce Obasanjo ba shi da hurumin sukar wata gwamnati a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng