Shugaban NNPP Ya Rasu ana Tsaka da Shirin Bikin Yar Kwankwaso
- Rahotanni da suka fito daga jihar Jigawa na tabbatar da cewa shugaban jam'iyyar NNPP a jihar ya rigamu gidan gaskiya
- Jagoran NNPP a Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne ya sanar da rasuwar Alhaji Mukhtari Ibrahim Gagarawa
- An ruwaito cewa Alhaji Mukhtari Ibrahim Gagarawa ya kasance gogaggen dan siyasa a jihar Jigawa kafin ya koma ga Allah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Jam'iyyar NNPP da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ke jagoranta ta tafka babban rashi.
Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Jigawa, Alhaji Mukhtari Ibrahim Gagarawa ya koma ga mahaliccinsa.
Jagoran NNPP a Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne ya sanar da rasuwar Alhaji Mukhtari Ibrahim Gagarawa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban NNPP a Jigawa ya rasu
A yau aka sanar da rasuwar shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Jigawa, Alhaji Mukhtari Ibrahim Gagarawa.
Alhaji Mukhtari Ibrahim Gagarawa ya kasance dan siyasa gogagge kuma ya rike mukamai daban daban.
Kwankwaso ya yi jajen rasuwar Gagarawa
Jagoran NNPP a Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya nuna takaici bisa rasuwar shugaban jam'iyyar.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce rasuwar Alhaji Mukhtari Ibrahim Gagarawa ta taɓa zuciyar mutane da dama.
"Ina mika sakon ta'aziyya ga NNPP a jihar Jigawa bisa rasuwar shugaban jam'iyyar, Alhaji Mukhtari Ibrahim Gagarawa.
Lallai iyalansa za su ji zafin rashin, haka zalika sauran abokan gwagwarmayarsa da dukkanmu baki daya."
- Rabi'u Musa Kwankwaso
Bayan shugabancin NNPP, shugaban ya taba rike matsayin shugaban karamar hukumar Gagarawa.
A karshe, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi addu'ar Allah ya gafarta wa marigayin kurakuransa ya kuma sanya shi a aljanna.
Za a daura auren yar Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa manyan baki sun fara isa Kano domin shaida auren yar Sanata Rabi'u Kwankwaso da za a daura a gobe Asabar, 16 ga watan Nuwamba.
Tsofaffin gwamnoni daga jihohi daban daban sun isa Kano yayin da jagoran NNPP ya karɓe su a gidansa bayan kammala sallar Juma'a.
Asali: Legit.ng