Wani Matashi Ya Yi Kaca Kaca da Darasin Lissafi, Ya Kafa Tarihi a Jami'ar Arewa
- Wani matashi da ya karanci darasin lissafi a Jami'ar Ilorin da ke Kwara ya samu sakamako mai daraja ta ɗaya da lambar yabo
- Ɗalibin ya wallafa sakamakon da ya samu a soshiyal midiya bayan ya kammala karatun digirin farko a wannan makaranta
- Ya kammala karatu da jimullar maki 4.97 ma'ana dai ya samu sakamako mai daraja ta farko a jami'a watau 'First Class'
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ilorin, Kwara - Wani haziƙin matashi ya kammala karatun digiri na farko a Jami'ar Ilorin ta jihar Kwara da sakamako mai ban sha'awa.
Matashin ya karanci darasin lissafi kuma ya yi kaca-kaca da shi, inda ya gama da sakamako mai daraja ta ɗaya watau 'First class'.

Asali: Twitter
Bayan ƴa karɓi satifiket ɗinsa, haziƙin matashin mai suna Ayodeji Akinsanya ya garzaya kafafen sada zumunta inda ya wallafa nasarar da ya samu a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasarorin da matashin ya samu a UNILORIN
A cewar Ayodeji, ya kammala karatunsa ne da maki CGPA na 4.97 sannan kuma shi ne dalibin da ya fi kowane ƙoƙari a shekarar a fannin lissafi.
Har ila yau Ayodeji ya zama ɗalibi mafi hazaƙa da kokari a gaba ɗaya Jami'ar Ilorin a wannan shekara.
Sannan kuma an ba shi lambar yabo a matsayin ɗalibi mafi hazaƙa a tsangayar kimiyya a UNILORIN.
Ayodeji ya lissafa nasarorin da ya samu kamar haka:
"Darasin lissafi 4.97/5.00
Za a buga takarduna uku,
ɗalibi mafi hazaƙa a fannin lissafi,
tsangayar kimiyya da kuma ɗalibin da ya gama karatu da sakamako mafi kyau a jami'a."
Martanin wasu mutane kan nasarar matashin
@phychem11 ya ce:
"Wasu mutanen ba su gajiya da karatu, ina taya ka murna Ayo."
@mubby249 ya ce:
"Ina taya ka murna ɗan uwa."
@Hakeem_Onitolo ya ce:
"Ina tayaka murna ɗan uwa, ka yi nasara babba. Kai tauraro ne kuma yanzu ka fara haskawa."
Mace ta kafa tarihi a Jami'ar Babcock
Ku na da labarin wata matashiya ‘yar Najeriya ta kafa tarihi a jami’ar Babcock, Ilishan-Remo bayan kamala digiri dinta.
Dalibar ta kamala digirin farko a kimiyyar na’ura mai kwakwalwa tare da samun makin 5.0 GPA a shekarar karshe.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng