Tsadar Rayuwa: An Tura Saƙo ga Buhari a Madadin Talakawan Najeriya

Tsadar Rayuwa: An Tura Saƙo ga Buhari a Madadin Talakawan Najeriya

  • Al'ummar Najeriya na cigaba da kokawa kan yadda tsadar rayuwa ke cigaba da barazana ga al'amuran yau da kullum na mutane
  • Wani mai wasan barkwanci a Kudancin Najeriya, Nosa Afolabi da aka fi sani da Lasisi ya tura wani sako ga Muhammadu Buhari
  • Legit ta tattauna da wani dan APC, Muhammad Isa domin jin ko ya yi kewar Buhari kasancewar jam'iyyarsu ke mulki har yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shahararren mai wasan barkwanci a Najeriya, Nosa Afolabi ya tura sako ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Buhari
Lasisi ya tura sako ga Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Nosa Afolabi ya ce ya tura saƙon ne a madadin dukkan talakawan kasar nan.

Kara karanta wannan

An fayyace wanda ke rike da Najeriya bayan ficewar Tinubu da Kashim daga kasar

Nosa Afolabi da aka fi sani da Lasisi ya tura sako ga Buhari ne kan halin rayuwa da al'ummar Najeriya ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakon talakawa da shugaba Buhari

The Cable ta wallafa cewa Nosa Afolabi ya tura sako ne ta hanyar murya ga Muhammadu Buhari, ya ce ana matuƙar kewarsa.

Bayan haka mai wasan barkwancin ya ce idan ya tuna yadda yake kewar Muhammadu Buhari sai ya ji kamar zai yi kuka.

Sakon da ya tura ya tayar da kura a kafafen sadarwa inda mutane suka rika bayyana ra'ayoyi mabanbanta. Ga sakon da Lasisi ya tura ga Buhari:

Ina tura maka wannan sakon ne a madadin kowa da kowa (a Najeriya), har da ni kaina da iyalina.
Ban taba tsammanin zan tura maka sako irin wannan ba a daidai wannan lokacin.
Har na rasa yadda zan bayyana maka abin da ke cikin raina, kawai dai ina mai tabbatar maka muna kewarka.

Kara karanta wannan

'Kamar ana yakin basasa,' Tsohon minista ya gargaɗi Tinubu, yana fargabar kaurewar rikici

- Lasisi

Bayan sakon, wasu a kafafen sada zumunta sun ce sun yi kewar Buhari wasu kuma sun ce a lokacinsa ma akwai tarin matsaloli a kasar nan.

Legit ta tattauna da Muhammad Isa

Wani mazaunin Pantami a jihar Gombe kuma dan jam'iyyar APC ya zantawa Legit cewa dole yan Najeriya su yi kewar Buhari.

Muhammad Isa ya ce duk da cewa APC ke mulki amma salon Buhari ya fi sauki da yan kasa a kan salon Bola Tinubu.

An gargadi Tinubu kan yunwa a Najeriya

Tsohon ministan gidaje Cif Nduesse Essien ya gargadi shugaba Bola Tinubu kan yunwa a Najeriya kamar yadda aka rahoto.

Cif Nduesse Essien ya ce idan yunwa ta yi yawa a tsakanin talakawa za ta iya haifar da munanan fada a fadin Najeriya.

A karkashin haka ya buƙaci Bola Tinubu ya canja tsare tsaren da ya kawo Najeriya ko talakawa za su samu sauki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng