‘Ita ce Ta Farko,’ Tinubu Ya Taya Yar Arewa da Ta Kafa Tarihi Murna
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Dr. Zainab Shinkafi Bagudu murnar zama shugabar kungiyar UICC ta duniya
- Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa zaben Zainab da aka yi ya nuna kwarewa da basira da take da shi a harkokin lafiya
- UICC ta shahara da yaki da cutar kansa kuma tana da kungiyoyi sama da 1,000 a karkashinta a kasashen duniya kusan 200
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya uwargidan tsohon gwamnan jihar Kebbi murna kan tarihi da ta kafa a nahiyar Afirka.
A ranar 8 ga watan Oktoba aka zabi Dr Zainab Shinkafi Bagudu ta shugabanci kungiyar UICC a fadin duniya.
Hadimin shugaban kasa a harkar sadarwa, Bayo Onanuga ne ya wallafa sakon taya murnar a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya taya yar Arewa murna
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Dr Zainab Shinkafi Bagudu murnar zama shugabar kungiyar UICC ta duniya.
Bola Tinubu ya ce zaɓen Dr Zainab ta jagoranci kungiyar duniya ya nuna irin dimbin mutane masu basira da Allah ya samar a tarayyar Najeriya.
Yadda yar Arewa ta kafa tarihi a Afrika
Dr Zainab ita ce mace ta hudu a dukkan fadin duniya cikin mutane da dama da suka rike shugabancin kungiyar UICC.
Haka zalika Dr Zainab ta kasance mace ta farko a nahiyar Afirka da aka zaba ta jagoranci kungiyar.
Manufar kungiyar UICC a duniya
Bincike ya nuna cewa an kafa kungiyar UICC ne a shekarar 1993 domin yaki da yaduwar cutar kansa a duniya.
Rahotanni sun nuna cewa akwai kungiyoyi sama da 1,100 a karkashin UICC a kasashe da biranen duniya dama dama da suka haura 179.
Wike ya fadi dalilin zaben Tinubu a 2023
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike ya yi magana kan zaben 2023.
Nyesom Ezonwo Wike ya ce bai yi nadama ba a kan yadda ya juya baya ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a zaben.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng