Sarkin Katsina Ya yi Babban Rashi, Gwamna Radda Ya Nuna Takaici

Sarkin Katsina Ya yi Babban Rashi, Gwamna Radda Ya Nuna Takaici

  • Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya rasa Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Hassan Kabir Usman
  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tura sakon ta'aziyya ga mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman
  • Haka zalika gwamna Dikko Umaru Radda ya yi kira na musamman ga al'umma kan koyi da halin kirki na Alhaji Hassan Kabir Usman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya rasa kaninsa, Hassan Kabir Usman.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya yi kira na musamman kan koyi da halayen marigayin yayin da ya tura sakon ta'aziyya.

Sarkin Katstina
Kanin sarkin Katsina ya rasu. Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da gwamnan ya yi ne a cikin wani sakon da jami'in gwamnatin Katsina, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar Sarkin Gobir, Sanata Tambuwal ya tafka babban rashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ya rasu a masarautar Katsina

Daily Trust ta wallafa cewa Alhaji Hassan Kabir Usman wanda ya kasance ƙani ne ga sarkin Katsina ya rasu yana da shekaru 55.

Haka zalika, Alhaji Hassan Kabir Usman shi ne mai rike da sarautar Sarkin Dawakin Tsakar Gida a masarautar Katsina.

Dikko Radda ya yi ta'aziyyar ƙanin sarki

Gwamna Umaru Radda ya isa fadar sarkin Katsina domin isar da sakon ta'aziyyar babban rashin.

Dikko Umaru Radda ya yi kira na musamman kan yin addu'a ga marigayin inda ya ce ya bar giɓi babba a jihar Katsina.

Koyi da halin kanin sarkin Katsina

Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce marigayin ya yi aiki tukuru wajen wanzar da zaman lafiya da cigaba a Katsina.

A karkashin haka ya ce ya kamata al'umma su yi koyi da halayensa na gari da ayyukan alheri da ya yi a lokacin rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bauchi ta shiga jimamin rasuwar sarkin Ningi, an fado gudunmawarsa

Gwamna Dikko Radda ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin tare da ba ilayansa da yan uwa hakuri.

An kashe dan sa kai a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa rashin tsaro na sauya salo a Katsina, miyagu sun kai hari har gidajen jami'in sa kai, tare da yi masa kisan gilla.

An ruwaito cewa miyagun sun kai harin rashin imani gidan Aliyu Yahaya da ke cikin kungiyar mafarauta a jihar, inda su ka kashe shi har lahira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng