Shahararrun Yan Gwagwarmaya da Ke Adawa da Zanga Zanga Bayan Shiga Gwamnatin Tinubu
- Yayin da kwanakin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa ke kara matsowa, jami'an Bola Tinubu na kara jawabi ga al'umma
- An samu wasu daga cikin jami'an gwamnatin Tinubu da a baya suke gaba gaba a zanga zanga amma suka juya baya a yanzu
- A wannan rahoton, Legit ta tattaro muku jerin jami'an gwamnatin da matsayin da shugaba Bola Tinubu ya ba su a cikin gwamanti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Nigeria - Duk da kira da jami'an gwamnatin Bola Tinubu ke yi ga matasa kan ajiye zanga zanga, matasan na nuna rashin yarda.
Wasu daga cikin matasan Najeriya sun zargi jami'an gwamnatin da cewa sun ki shiga zanga zanga ne saboda ana damawa da su a yanzu.
A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku sunayen wasu shahararrun yan gwagwarmaya da ke adawa da zanga zanga bayan shiga gwamnati.
1. Dada Olusegun ya soki zanga zanga yau
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa tsohon dan gwagwarmaya, Dada Olusegun ya yi gargadi ga masu shirin fita zanga zanga da cewa magoya bayan Tinubu ba za su kyale su ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai a lokacin da shugaba Goodluck Jonathan ya cire tallafin mai Dada Olusegun ya kasance na gaba gaba a fita zanga zanga.
A yanzu haka Dada Olusegun na cikin masu taimakawa shugaba Bola Tinubu a kan harkokin yada labarai.
2. Abdulaziz: 'Na yi zanga zanga a baya'
Abdulaziz Abdulaziz ya ya wallafa a Facebook cewa ba zai shiga zanga zangar da ake shirin yi ba saboda akwai alamar tarzoma a cikinta.
Haka zalika ya bayyana cewa a shekarun 2014 da 2012 ya shiga zanga zanga saboda akwai tsari a wancan lokacin.
Shugaba Bola Tinubu ya ba Abdulaziz Abdulaziz mukami a matsayin mai taimaka masa a harkokin sadarwa.
3. Rahma Abdulmajid da zanga zanga
Rahma Abdulmajid ta kasance cikin wadanda suka jagoranci zanga zanga a gwamnatocin Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari.
Amma a wannan karon ta wallafa a Facebook cewa zanga zanga ba wajibi ba ne a kan kowa idan wasu suka yi wasu za sun dauke musu.
Rahma Abdulmajid ta kasance cikin masu taimakawa shugaba Bola Tinubu a harkar sadarwa musamman a kafafen rediyo.
Ndume: Matasa sun yi zanga zanga a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar matasa a jihar Borno sun gudanar da zazzafan zanga zanga a birnin tarayya Abuja kan tsige Sanata Ali Ndume da majalisa ta yi.
Matasan sun gudanar da zanga zangar ne a dandalin Unity Fountain inda suka bayyana buƙatarsu ga shugaban majalisar dattawan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng