Notcoin: Dan Najeriya Ya Samu Naira Miliyan 9 Daga Haƙar Ma’adanan Crypto a Wayarsa

Notcoin: Dan Najeriya Ya Samu Naira Miliyan 9 Daga Haƙar Ma’adanan Crypto a Wayarsa

  • Wani dan Najeriya da ya ci gajiyar sabon mining na Notcoin da aka kammala kuma aka shigar da shi kasuwa ya yi murnar kudin da ya samu
  • Mai bincike kan harkar crypto kuma marubucin ya bayyana cewa ya samu zunzurutun kudi har Naira miliyan tara daga da'awar Notcoin
  • Kwararre a fannin kasuwancin crypto, Nura Haruna, da ya zanta da Legit Hausa, ya yi magana kan tasirin mining a tsakanin matasan Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Daya daga cikin wadanda suka cin gajiyar Notcoin, Tola Joseph Fadugbagbe, ya nuna farin ciki na samun Naira miliyan tara daga hakar ma'adanan crypto.

Dan Najeriya ya yi murnar samun Naira miliyan 9 daga Notcoin
Tola Joseph Fadugbagbe ya samu Naira miliyan 9 daga hakar ma'adanan Notcoin. Hoto: @connectwithtola, Bitcoin News
Asali: Twitter

Matashi ya samu N9m a Notcoin

Marubucin ya je shafinsa na X inda ya wallafa irin nasarar da ya samu ta hanyar daddana kwandalar Notcoin a Telegram yayin da ya nemi mabiyansa su fadi masa abin da suka samu.

Kara karanta wannan

"An gyara zalunci": 'Dan Sanusi II ya magantu da majalisa ta rusa masarautun Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai babu wanda ya tabbatar da wannan da'awa da matashin ya yi a shafinsa.

Tola Fadugbagbe, ya wallafa cewa:

“Na samu N9m a kyauta bayan an shigar da Notcoin kasuwa.
"Nawa kuka samu?
"Kowa ya zo ya yi murnar nasar da ya samu."

Duba abin da ya rubuta a kasa:

Abin da Binance ya ce kan Notcoin

A cewar kamfanin Binance, Notcoin (NOT) wani sulallan crypto ne da aka samar da shi a tsarin 'ka shiga manhajar ka tara sulallan NOT' a kan Telegram.

Notcoin ya ba wa mutane damar "hakar" ma'adan kudin na intanet ta hanyar daddana wata kwandala da za ake gani idan an bude manhajar a Telegram.

Makomar mining a tsakanin matasan Najeriya

A zantawarsa Legit Hausa da wani masani kan harkar crypto, Nura Haruna Maikarfe, wanda ya fara da cewa an kirkiro mining ne domin jawo hankalin masu saka hannun jari na duniya kan wani 'project' na crypto.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya boye N1m da aka tura masa bisa kuskure wajen aiko sadakar N100, 000

A yayin da hakar ma'adanan crypto ke ba mutane damar tara sulalla tare da zama kudi idan an kai shi kasuwa, sai dai Nura Maikarfe ya ce harkar mining na da hadari ga al'ummar Najeriya.

A cewar masanin:

"Najeriya ta fi ko ina yawan raja'a kan mining a duniya, kuma mafi akasarin masu shiga ba su da ilimi kan harkar crypto, wannan zai ba da sauki wajen ba su kudi ta hannun dama a karbe ta hannun hagu.
"Matasa da dama sun ajiye sana'o'insu, ko aikinsu, sun rungumi harkar mining, wannan ma wata matsala ce da za ta iya shafar zamantakewa da tattalin arzikin jama'a da kasa.
"Akwai bukatar gwamnati ta bullo da tsari na sa ido kan harkokin mining, wannan zai kare 'yan kasa daga fadawa komar 'yan damfara da kuma ba gwamnati kudaden shiga."

Abin da ya sa Tapswap ya daina aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa mutane sun yi ta korafe-korafe bayan manhajar hakar ma'adanan crypto ta Tapswap ta daina aiki.

Kara karanta wannan

Hallaccin 'Mining': Abin da malamin musulunci ya ce game da Notcoin da TapSwap

Wadanda suka kirkiri Tapswap sun ba al'uma hakuri kan wannan tangardar da aka samu yayin da kuma suka sanar da irin kokarin da suke yi a kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel