"Idan a Afirika Ka Ke Za Ka Iya Jaraba Sa'a": Samari Sun Yi Rububin Baturiyar Da Tace Tana Son 'Yan Afirika
- Wata baturiya ta bayyana cewa tana son nahiyar Afirika inda tace nahiyar kamar Aljannah take, wanda hakan ya janyo mutane suka yi ta sharhi a TikTok
- Baturiyar mai suna Raistii, ta bayyana cewa tana son ziyarar ƙasashen Afirika irinsu Najeriya, Uganda da Kenya domin tana matuƙar son su
- Raistii ta mayar da martani kan wata tambaya da wani ya yi mata ko tana da saurayi, inda tace samari daga Afirika za su iya neman soyayyarta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata baturiya ta bayyana irin son da take yi wa nahiyar Afirika, inda ta bayyana nahiyar a matsayin Aljannah.
Baturiyar mai suna Raistii, ta bayyana cewa za ta so ta ziyarci ƙasashen Afirika da dama irinsu Najeriya, Uganda da Kenya.
Raistii tana da shafi a TikTok wanda mutum 588k ke bibiyarta inda bidiyoyinta sun samu 'likes' sama da 4m.
Bayan Taro a Aso Villa, NLC Ta Yi Magana Kan Janye Zanga-Zanga da Shiga Yajin Aikin da Ta Shirya a Najeriya
A cikin ƴan kwanakin nan, ta yi wani bidiyo tana yabon nahiyar Afirika, inda ƴan Afirika suka yi ta yaba mata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cikin ɗaya daga cikin bidiyoyinta ta bayyana cewa:
"Suna yawan tambaya ta ƙasar da na fi so a Afirika. Ba zan iya zaɓa ba. Dukkaninsu suna da kyau. Afirika kamar Aljannah ce."
Ƴan Afirika za su iya neman soyayyar baturiya
A cikin wani bidiyon, an tambayi Raistii ko tana da saurayi ko ƙofa a buɗe take ga masu son neman soyayarta, inda tace ƙofa a buɗe take ga masu son jaraba sa'ar su.
A kalamanta:
"Idan daga Afirika ka ke, har yanzu akwai sauran gurbi domin ƴan Afirika, za ka iya jaraba sa'ar ka. Idan ba haka babu sauran ƙofa. Wannan shi ne kawai abinda ake buƙata.
Masu amfani da Tiktok sun yi tsokaci
Mutane da dama sun garzaya sashin bayani inda suka nuna suna son samun soyayyarta.
@Eliyh Elickz ya rubuta:
"Tana nufin ƴan Afirika ƴan Kenya da Uganda, sauran ku shiga taitayinku."
@Xaji Yoow ya rubuta:
"Cikin girmamawa da ladabi da biyayya, a shirye na ke na kasance cikin rayuwarki.
Bidiyon 'Yar Najeriya Na Talla a Turai Ya Dauki Hankula
A wani labarin kuma, wata ƴar Najeriya ta ɗauki hankula a yanar gizo bayan bidiyonta yana bayyana tana tallar ruwa a nahiyar Turai.
Ƴar Najeriyar dai ta koma Turai ne domin samun ingantacciyar ruwa, sai ga shi ta koma tana tallar ruwan roba a bakin titi.
Asali: Legit.ng