Karamin Yaro Ya Hakikance Mahaifinsa Bai Mutu Ba a Wajen Binne Gawa, Bidiyon Ya Yadu

Karamin Yaro Ya Hakikance Mahaifinsa Bai Mutu Ba a Wajen Binne Gawa, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani ƙaramin yaro ɗan Najeriya ya yaɗu sosai a soshiyal midiya bayan ya haƙiƙance cewa mahaifinsa da ya kwanta dama yana raye
  • A cikin wani bidiyo dake tashe, wani mutumi ya yi wa yaron tambayoyi a wajen binne gawar mahaifinsa da ya mutu
  • Lokacin da aka tambaye shi kan mutuwar mahaifin nasa, ƙaramin yaron ya bayyana cewa an binne masa mahaifi yana raye

Bidiyon wani ƙaramin yaro ɗan Najeriya a wajen binne gawar mahaifinsa ya yaɗu sosai a yanar gizo.

A cikin bidiyon mai sosa zuciya wanda wani mai amfani da sunan @vibewithmyg a TikTok ya sanya, an tambayi ƙaramin yaron yadda yake ji dangane da mutuwar mahaifinsa.

Karamin yaro ya hakikance mahaifinsa bai mutu ba
Karamin yaron ya hakikance mahaifinsa na da rai Hoto: @vibewithmyg
Asali: TikTok

Sai dai, ƙaramin yaron a cikin bidiyon ya haƙiƙance cewa mahaifinsa bai mutu ba, inda ya ce sun binne shi ne da ransa.

Kara karanta wannan

‘Ba Batun Neman Minista Ba Ne’, Jonathan Ya Bayyana Dalilin Kai Wa Tinubu Ziyara

Da aka tambaye shi dalilin da ya sanya yake jin mahaifinsa na raye, ƙaramin yaron ya bayyana cewa mahaifinsa da yanzu yana raye da basu binne shi ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Sun yi ƙarya cewa mahaifina ya mutu. Mahaifina bai mutu ba. Ku tayar da shi za ku gani. Idan kuka buɗe za ku ga bai mutu ba, zai miƙe." A cewarsa.

Sharhin da ƴan soshiyal midiya suka yi akan bidiyon

@mimi_hair1 ta rubuta:

"Haka nima nayi lokacin da mahaifina ya mutu. Ina can ina ta tsintsar marafan kwalbar lemu da zan yi amfani da su wajen yin ƙirga a makaranta. Ina ta tiƙar rawa da cin shinkafa.

@ijiugo ya rubuta:

"Omooooooooooo. Wannan ya sanya hawaye sun zubo daga idanuna, Wo! kuka kawai na ke. A lokacin binne mahaifina, ban taɓa yarda cewa ya mutu ba har sai da aka ce na watsa masa ƙasa."

Kara karanta wannan

Bidiyon Davido: Hadimin Mawaƙin Ya Goge Rubutun Neman Afuwa Da Ya Yi Yayin Da Ya Ƙi Bai Wa Musulmai Haƙuri

@darlington912 ya rubuta:

OMO ina a irin wannan shekarun ne mahaifina ya rasu, nima a lokacin murna ta kawai nake a cewar mahaifiyata."

@ugoxhukwu ya rubuta:

"Mutanen dake ganin laifin wanda yake masa tambayar, idan basu gaya masa gaskiya ba a wannan shekarun zai yi wahala ya san gaskiya duk lokacin da ya tuna da binne gawar."

Matashi Ya Kwashe Shekaru Yana Neman Iyayensa

A wani labarin kuma, wani matashi ya koka kan rashin ganin iyayensa da ya yi tun yana ɗan wata biyar a duniya.

Matashin ya bayyana cewa shekararsa 29 yana neman iyayensa amma har yanzu babu labari, sai dai ya ce ba zai taɓa cire rai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng