Amarya Ta Soke Bikinta Ana Saura Sati Daya Saboda Ango Baya Da Kudin Biyan Shagulgula Da Za Ayi
- Wata budurwa mai shirin zama amarya ta soke aurenta ana saura sati ɗaya biki saboda angon ba zai iya ɗaukar nauyin shagulgula biyar ba
- Ƴan uwa da ƙawayenta sun fusata matuƙa kan abinda ta aikata duk da shawarwarin da suka bata na ta haƙuri ayi bikin
- Mutane da dama sun taya ango murna ya kaucewa aikata aikin da na sani na auren mai son abun duniya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata budurwa da ake shirin aurenta ta sanya iyayenta da ƴan uwanta cikin baƙin ciki bayan ta soke bikinta ana saura sati ɗaya a ɗaura aure.
Wani mai amfani da sunan @Galadanci02 a Twitter, shi ne ya kawo labarin inda ya ce amaryar tana son a raƙashe da shagulgula har guda biyar a bikin nata, lamarin da angon ya ce sam ba za a yi haka da shi ba saboda baya da kuɗin ɗaukar nauyinsu.
An shirya za a gudanar da bikin na su ne a ranar 30 ga watan Yulin 2023, amma sai wannan taƙaddamar ta faɗo a tsakaninsu kan kuɗin da za a kashe a wajen bikin.
Angon ya gaya mata cewa ta ƙyale duk wasu abubuwan shagulgula da ta shirya ta mayar da hankali kan bikin, amma sai ta ƙeƙasa ƙasa tace ita ba haka ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amaryar ta ƙi yarda ta haƙura kada ayi shagulgulan
Iyayen amaryar da ƙawayenta duk sun bata baki domin ta haƙura a gudanar da bikin haka nan, amma tace sam bata yarda ba.
An nuna mata cewa shagulgula basu ba ne abubuwa masu muhimmanci a aure ba, inda suka shawarceta da ta mayar da hankali kan abubuwa masu muhimmanci da su ke a cikin aure.
An kammala shirya komai
Dukkanin wasu shirye-shiryen bikin da za ayi duk an kammala su, domin har kayan lefe an riga da an kawo gidansu amarya, ranar biki kawai ake ta jira.
Da Dumi-Dumi: 'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Gidan Tsohon Minista a Najeriya, Sun Tafka Barna
Ƙawayen amarya sun cire kuɗi sun yi anko domin wasu daga cikinsu har sun karɓo daga wajen masu ɗinki, inda suka yi Allah ya isa saboda asarar kuɗi da ta janyo musu.
Mutane da dama da suka yi sharhi sun taya angon murnar kaucewa aikata aikin dana sani domin a cewarsu, budurwar tabbas ba matar da za ayi farin cikin aura ba ce.
Magidanci Ya Koka Bayan Matarsa Ta Ki Bari Su Raya Sunnah
A wani labarin na daban kuma wani magidanci ya koka kan yadda matarsa ta ƙi ba shi haƙƙinsa na zamantakewar aure dake a tsakaninsu.
Magidancin dai ya kwashe shekara uku ba tare da sanin cewa ya yi aure ba domin matarsa ta yarda su raya Sunnah.
Asali: Legit.ng