Mai Kitso Ta Yi Wa Budurwa Aski Saboda Ta Ki Biyan Kudin Kitso, An Tafka Mahawara Kan Bidiyon

Mai Kitso Ta Yi Wa Budurwa Aski Saboda Ta Ki Biyan Kudin Kitso, An Tafka Mahawara Kan Bidiyon

  • Wata budurwa ta sanya kanta cikin matsala bayan ta ƙi biyan kuɗin kitson da aka yi mata a wajen wani shagon gyaran gashi a ƙasar Afirika ta Kudu
  • Wani mai amfani da sunan @AdvoBarryRoux a Twitter, ya sanya bidiyon yadda mai kitson ke aske gashin budurwar saboda ta ƙi biyanta haƙƙinta
  • A cewar labarin, budurwar ra nemi da ayi mata kitso na gani na faɗa duk kuwa da ta san cewa ba ta da kuɗin biya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata budurwa a ƙasar Afirika ta Kudu ta zama abin magana bayan ta jefa kanta cikin cakwakiya a shagon gyaran gashi.

Lamarin dai ya fara ne lokacin da wani mai amfani da sunan @AdvoBarryRoux ya sanya bidiyon musayar kalamai masu zafi da aka yi a tsakanin mai yin kitso da budurwar da ta je ayi mata kitso.

Kara karanta wannan

"Kada Ki Bari A Kama Ki": Dalibar Jami'a Ta Nuna Salon Satar Jarabawa a Soshiyal Midiya Cikin Izza, Bidiyon Ya Yadu

An yi wa budurwa aski saboda kin biyan kudin kitso
An rantale kan budurwar saboda kin biyan kudin kitso Hoto: @AdvoBarryRoux
Asali: Twitter

Dalilin musayar kalaman na su dai shi ne, wacce aka yi wa kitson ta ƙi biyan kuɗin kitson da ta ce ayi mata duk da ta san cewa babu kuɗin da za ta biya kitson da aka yi mata.

Mai kitson ta fusata inda ta yi wa budurwar aski

Bidiyon ya nuna mai kitson tana amfani da wani abu wanda ya yi kama da reza wajen aske gashin kan budurwar, inda ta yi mata rantali a kan nata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da bidiyon ya yaɗu a kafafen sada zumunta, mutane da dama sun yi ta bayyana mabanbantan ra'ayoyi akan lamarin.

Ga bidiyon nan ƙasa:

Ga wasu daga cikin waɗanda Legit.ng ta tattaro:

veseverah ta rubuta:

"Wannan ba a kyauta ba amma abun dariya ne. Yana da kyau mutum ya riƙe gaskiyarsa kada ya yi tunanin ƙarya domin yaudarar mutane za ta sanya ya zama yafi kowa wayau."

Kara karanta wannan

"Ta Sauya Lambobinta": Bayan Gama Lashe Kudin Saurayin Da Ya Dauki Nauyin Karatunta, Budurwa Ta Auri Wani Daban

natura__essie ta rubuta:

"Kamata ya yi ta warware kitsonta ko ta kai ta wajen ƴan sanda.... mai ta ke taƙama da shi da za ta aske mata gashi? Ha! ku kuma masu son yin kitso ba ku da kuɗi menene matsalarku? Wa ku ke son birgewa? Idan ba ku da kuɗi ku tattara shi waje ɗaya kawai."

thefoodnetworknig2 ya rubuta:

"Na tausayawa mutanen da suka ɓata ran mai kitson nan... Zuciyarta irin ta ƙarfe ce."

egoumez ta rubuta:

"Kallon bidiyon nan ya sanya ni kuka. Dubi wannan cin mutuncin. Eh ba ta kyauta amma ai da warware kitson suka yi sannan su yi mata hukunci."

Budurwa Ta Bar Saurayinta Da Cizon Yatsa

A wani labarin kuma, wata budurwa ta yaudari saurayinta da ya yi ɗawaoniya da ita har ta kammala karatunta.

Budurwar dai ta sulale ta koma ƙauye da inda ta auri wani daban ta bar saurayin na ta da cizon yatsa cikin takaici.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng