Budurwa Ta Guji Saurayin Da Ya Yi Dawainiya Da Ita, Ta Auri Wani Daban

Budurwa Ta Guji Saurayin Da Ya Yi Dawainiya Da Ita, Ta Auri Wani Daban

  • Wani matashi ɗan Najeriya ya ɗauki nauyin karatun budurwarsa inda ya tabbatar ta kammala ba tare da wata matsala ba
  • Bayan ta kammala karatun na ta, matashin ya siyo mata sabuwar mota ƙirar Toyota sannan ya kama mata hayar gida mai ɗaki biyu
  • Abubuwa sun taɓarɓare masa ne lokacin da budurwar ta yi tafiya zuwa ƙauyensu wacce bata dawo ba saboda ta auri wani daban wanda yake aikin gyaran wutar lantarki

Wata budurwa ƴar Najeriya ta watsawa saurayinta ƙasa a ido wanda ya ɗauki nauyin karatunta, inda ta je ta auri wani daban.

Wani mai amfani da sunan @_agneeess a manhajar Twitter ya bayyana yadda budurwar ta bar saurayinta da ke zaune a cikin birnin ta koma ƙauye ta auri wanda yake sana'ar gyaran wutar lantarki.

Kara karanta wannan

"Ya Daina Cin Abinci Na": Matar Aure Ta Bari Garjejen Kato Ya Yi Mata Tausa, Mijinta Ya Fusata Matuka

Budurwa ta rabu da saurayin da ya yi dawainiya da ita
Budurwar tace ba saduwa kafin aure amma ta je wani daban ya yi mata ciki Hoto: Getty Images/ Caia Image and Djavan Rodriguez.
Asali: Getty Images

Budurwar tace ba saduwa da juna har sai an yi aure

A lokacin da su ke soyayya da matashin, budurwar ta haƙiƙance cewa ba za su ɗanɗani daɗin juna ba kafin aure, inda matashin ya amince da wannan sharaɗin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matashin ya tabbatar da cewa ba ta samu matsalar kuɗi ba a tsawon shekarun da ta kwashe a makaranta kafin ta kammala.

Yadda budurwa ta rabu da saurayinta bayan ya gama biya mata kuɗin makaranta

Haka kuma bayan ta kammala karatunta, matashin ya siyo mata sabuwar mota ƙirar Toyota sannan ya kama mata hayar gida mai ɗaki biyu.

Amma matsalar ta fara ne lokacin da budurwar ta yi tafiya zuwa ƙauyensu inda ta ƙi dawowa wanda daga ƙarshe kuma ta samu juna a biyu.

Wani ɓangare na labarin na cewa:

"Yanzu mutuminka shi ga damo sarki haƙuri, ya ci gaba da jiran dawowarta. A satin da wuce, an samu sabbin abubuwa. Ya ga hotunan baikonta a WhatsApp ɗin tsohuwar wacce suka zauna ɗaki ɗaya tare. Tana da cikin wata uku a lokacin yin baikon. Ta sauya dukkanin lambobin wayarta, ta siyar da motar ta yi amfani da kuɗin wajen ɗaukar nauyin auren. Mutumkinka yaje gidan da ya kama mata haya ya tarar ta bayar da hayarsa cikin sauki ta yi gaba da kuɗin."

Kara karanta wannan

An Sanya Dokar Bulala 40 Ko Tarar 10,000 Kan Duk Budurwar Da Ta Yi Shigar Banza a Wani Yankin Najeriya

Budurwa Ta Koka Bayan Saurayin Da Ta Yi Wa Yanga Ya Auri Wata Daban

A wani labarin kuma, wata budurwa ta shiga cikin matuƙar damuwa bayan saurayin da ta tsaya yi wa yanga ya auri wata daban.

Budurwar dai ta yi arba ne kwatsam da hotunan saurayin bayan ta nuna masa cewa ba ta sonsa. Ganin hotunan bikinsa ya sanyata shaɓar kuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng