"Na Yi Asara": Budurwa Ta Koka Bayan Ta Yi Arba Da Hotunan Auren Saurayin Da Ta Tsaya Yi Wa Jan Aji

"Na Yi Asara": Budurwa Ta Koka Bayan Ta Yi Arba Da Hotunan Auren Saurayin Da Ta Tsaya Yi Wa Jan Aji

  • Wata budurwa ƴar Najeriya ta sharɓi kuka bayan ta gano cewa saurayin da ya nuna yana son ta ya auri wata daban
  • A bidiyon wanda ya yaɗu a Soshiyal midiya, budurwar ta yi kuka sosai lokacin da ta ke kallon hotunan ɗaurin aurensu
  • Masu amfani da Soshiyal midiya sun bayyana ra'ayoyinsu kan bidiyon inda da yawa daga cikinsu suka ba ta shawara ta nemi wani saurayin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata budurwa ƴar Najeriya ta shiga damuwa bayan ta gano cewa saurayin da ta daɗe tana yi wa jan aji ya auri wata daban.

An nuna budurwar cikin wani bidiyo tana ta kuka kan lamarin bayan ta gano cewa saurayin ya yi auren shi ya fita harkarta.

Budurwa ta sha kuka bayan ganin hotunan auren saurayin da ta yi wa jan aji
Budurwar na ganin hotunan auren sai ta barke da kuka Hoto
Asali: TikTok

A cewar majiyoyi, budurwar ta yi kaciɓus ne da hotunan auren saurayin ne a wayarta, wanda hakan ya sanya ta cikin kaɗuwa da baƙin ciki.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Auri Attajirin Da Yake Ba Ta N50k Duk Wata, Ta Yi Korafin Cewa Ya Cika Mako

Bidiyon ya sanya an yi ta tafka muhawara a sashin bayanai inda wasu suka nuna goyon bayansu kan abinda saurayin ya yi, yayin da wasu kuma suka yi iƙirarin cewa dama ba son ta yake ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ku kalli bidiyon a nan ƙasa:

An bayyana mabanbantan ra'ayoyi akan bidiyon

@sire___kezzy27 ya rubuta:

"Wato ya yi ta jiran ki ko yana neman soyayyar ki. Ba kowane namiji ba ne yake da lokacin hakan. Mutum na can na neman kuɗi kuma ya zo ya yi ta neman wacce za ta so shi. Tun da ya nuna buƙatarsa kika ƙi yarda, wacce ta karɓi tayinsa ai ita zai aura."

@youngest_d_love ya rubuta:

"Meyasa ƴan mata su ke son hakan ne su yi ta jan aji. Kaso 80% na samarin da za su tsaya ana musu jan aji bada gaske su ke ba dama. A lokuta da dama waɗanda da gasken su ke haƙura su ke saboda hakan shi ya fi."

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fasa Auren Attajirin Saurayinta Ana Dab Da Biki, Ta Bayyana Dalilanta a Cikin Bidiyo

@carphy_flinks ta rubuta:

"Mata kenan za a ce ana sonku ku tsaya yanga, kun ga duk waɗannan samarin basu da lokaci fa, idan suka ce suna son budurwa ta tsaya musu yanga, wucewa kawai za su yi wajen ta gaba. Ina taya wacce ta yi nasara murna."

@director.lui ya rubuta:

"Wasu ƴan matan basu sonka. Sannan kuma basu son wata ta same ka."

@_donnyboi ya rubuta:

"Za ku yi ta wahalar da samari."

Baturiya Na Neman Mijin Aure Ido Rufe

A wani labarin kuma, wata baturiya ta garzaya intanet neman wanda zai samo mata saurayin da za ta aura.

Kyakkyawar baturiyar ta bayyana cewa akwai tukwici mai tsoka ga duk wanda ya samo mata wanda ya aureta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng