Wata Yar Najeriya Ta Gwangwaje Mahaifiyarta Da Kyautar Sabuwar Mota, Bidiyon Ya Yadu a Intanet

Wata Yar Najeriya Ta Gwangwaje Mahaifiyarta Da Kyautar Sabuwar Mota, Bidiyon Ya Yadu a Intanet

  • Wata ‘yar Najeriya ta bai wa mahaifiyarta kyautar sabuwar mota, wacce ta maye gurbin tsohuwar motar da ta siya mata a baya
  • Matar ta ce kyautar motar ta haɗaka ce ita da mijinta, wacce a faifan bidiyo an ga lokacin da suke gabatar ma ta ita
  • Farin cikin da ta nuna a lokacin da ta amshi kyautar motar ya sanya mutane da dama tofa albarkacin bakunansu

Wata ‘yar Najeriya ta haɗa hannu da mijinta domin sayawa mahaifiyarta sabuwar galleliyar mota.

A wani faifan bidiyo da aka wallafa a TikTok ta shafin @funkycollectionz, ya nuna lokacin da matar da mijin na ta suke miƙawa mahaifiyarta kyautar motar.

Wata mata ta bai wa mahaifiyarta kyautar sabuwar mota
Mata ta gwangwaje mahaifiyarta da kyautar sabuwar mota. Hoto: @funkycollectionz
Asali: TikTok

Matar da mijinta sun yi wa mahaifiyar zuwan bazata

A cikin faifan bidiyon, an ga cewa mahaifiyar tana barci ne a lokacin da ɗiyar ta zo da sabuwar motar da za ta musanya ma ta tsohuwar da take amfani da ita.

Kara karanta wannan

"Babbar Kawata Za Ta Auri Mijina": Matar Aure Ta Koka Bayan Mijinta Ya Rabu Da Ita Saboda Ya Gama Lashe Albarkatunta

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An kuma ga lokacin da 'yar ta shiga dakin da mahaifiyar ta ta ke kwance, inda ta tashe ta kan ta fito waje don ganin abin mamakin da ke jiranta.

A yayin da ta fito daga ɗakin, ta cika da matuƙar mamaki da aka faɗa ma ta cewa yanzu ita ke da wannan sabuwar mota.

Cikin sauri ta shiga motar inda ta fara rera waƙoƙi na godiya ga Ubangiji sannan kuma ta rungume mijin diyar ta ta domin nuna matuƙar godiyarta.

Dan gajeren bidiyon, wanda ya narkar da zukata da dama, ya yi yawo sosai a kafar TikTok.

Masu amfani da TikTok sun tofa albarkacin bakinsu kan matar da ta siyawa mahaifiyarta mota

@Dee ya ce:

"Haka zan yi wa mahaifiyata kwanan na."

@mercysavage18 ya ce:

"Nima haka zan yi wa mahaifiya ta nan ba da jimawa ba."

Kara karanta wannan

"Ba Miji, Ba 'Ya'Ya": Wata Mata Mai Shekara 39 Ta Yi Kukan Rashin Samun Miji, Bidiyonta Ya Yadu

@Oliviamiya ta ce:

"Jajirtacciyar mahaifiya."

@Funke ya ce:

"Zan sanya mahaifiyata farin ciki."

@Omofonmwan Otasowie ya ce:

"Allah ya saka muku da alkhairi. Ina addu'ar Allah ya albarkace mu ni da 'yar uwata, mu sanya murmushi a fuskar iyayenmu."

Baturiya ta ɗau alƙawarin bayar da biza kyauta ga duk wanda zai aureta

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan wata baturiya da ta ja hankulan jama'a a Intanet bayan wallafa wani bidiyo na ta da aka yi a TikTok.

A cikin ɗan gajeren faifan bidiyon, an ga matar na bayyana cewa a shirye take ta bai wa duk wanda ya amince zai aureta kyautar biza da zai koma Turai da zama tare da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng