"Ba Miji, Ba 'Ya'Ya": Matashiya Ta Koka Kan Rashin Abokan Rayuwa

"Ba Miji, Ba 'Ya'Ya": Matashiya Ta Koka Kan Rashin Abokan Rayuwa

  • Wata mata mai shekara 39 a duniya ta garzaya Soshiyal midiya inda ta koka kan ƙalubalen da ta ke fuskanta a rayuwarta
  • Matar wacce ta yi hijira zuwa UK tace duk da shekarun da ta ke da su a duniya har yanzu ba ta da miji da ƴaƴanta na kanta
  • Labarin nata ya sosa zukatan mutane da dama a Soshiyal midiya inda ƴanmata, zawarawa da masu aure suka riƙa bayar da na su labarin gwagwarmayar

Wata mata ta koka a TikTok cewa har yanzu ba ta da saurayi ko miji duk da tana da shekara 39 a duniya.

A yayin da ta sanya wani bidiyo wanda ta ke ta sharɓar kuka, matar wacce ta yi hijira zuwa UK ta yi tsokaci kan wasu abubuwa da ke ci mata tuwo a ƙwarya a rayuwarta.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Rabu Da Mijinta Bayan Ta Samu N1.5bn, Kotu Ta Umarci Ta Ba Mijin Duka Kudin, Ta Bayar Da Kwakkwaran Dalili 1

Mata mai shekara 39 ta koka kan rashin miji
Matar ta sosa zukata sosai Hoto: @girl.from.the.vil
Asali: TikTok

Bayan rashin miji ko saurayi, ta bayyana cewa ba ta da ƴaƴa ko mota sannan ba ta da gidan kanta.

Bidiyon na ta mai sosa zuciya dai ya yaɗu a manhajar TikTok, inda sama da mutum 392k suka kalli bidiyon a lokacin haɗa wannan rahoton.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mata da yawa sun ƙarfafa mata guiwa da kalamai masu taushi da labarin rayuwarsu.

Mutane sun nuna goyon baya ga matar mai shekara 39

katohillary651 ta rubuta:

"Ni ma na kusa shekara 35 bani da gida ina gararamba ne kawai, yanzu haka an kore ni daga aiki amma ina da fatan cewa Allah zai taimake ni na fara gidan kai na Insha Allah."

Andy Yesican #major# ta rubuta:

"Ki daure ki yi iya bakin ƙoƙarinki ki haifi ko da yaro ɗaya ne.. idan auren bai samu ba.. shi ne abu mafi muhimmanci da zai faru da ke."

Kara karanta wannan

Tsadar Mai: Magidanci Ya Saki Daya Daga Cikin Matansa, Ya Mayar Da Dayar Gida Saboda Matsin Tattalin Arziki

user2080804434010 ya rubuta:

"Kina da kyau ƴar'uwa, za ki yi aure a wannan shekarar sannan ki haifi ƴaƴanki."

Tonia Omasan ta rubuta:

"Kada ki damu ƴar'uwa ki ci gaba nema wajen ubangiji zai baki fiye da abinda kike zato."

Wata Mata Ta Nemawa Yayanta Mijin Aure

A wani labarin kuma, wata mata ta garzaya yanar gizo nemawa ƴaƴanta mata kyawawa mazajen da za su auresu.

Matar ta koka cewa yaran suna ta girma amma har yanzu sun kasa samun waɗanda za su auresu. Ta tabbatar da cewa ƴaƴanta na sanyawa a gaban mota ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel