Matar Aure Ta Rabu Da Mijinta Bayan Ta Samu N1.5bn, Kotu Ta Umarci Ta Ba Mijin Duka Kudin
- Wata mata wacce ta samu kuɗin caca har N1.5bn ta ɓoye ba ta bari mijinta ya sani ba sannan ta sake shi daga baya ta samu hukuncin kotu
- Tsautsayi ne ya sanya mijin ya gano gaskiya daga baya bayan wata wasiƙa da aka turo inda kawai ya maka ta kotu
- Alƙalin kotun ya ba shi dukkanin kuɗaɗen da ta samu daga cacar inda ya ce ta yi zamba cikin aminci da damfara
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata mata a ƙasar Amurka za ta rabu da kuɗaɗenta har N1.5bn da ta ciyo a caca ga tsohon mijinta bayan ta ɓoye masa cewa tana da kuɗin a lokacin da za su rabu.
Matar mai suna Denise Rossi, ta ciyo kuɗin ne a caca kwanaki 11 kafin ta nemi saki a wajen mijinta Thomas Rossi, wanda suka kwashe shekara 25 tare.
Tsadar Mai: Magidanci Ya Saki Daya Daga Cikin Matansa, Ya Mayar Da Dayar Gida Saboda Matsin Tattalin Arziki
Kotu ta ba mijin nasara
Denise ba ta gayawa mijinta ko kotun maƙudan kuɗaden da ta lashe ba, inda ta yi gum da bakinta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai, reshe ya juye da mujiya lokacin da wata wasiƙa daga kamfanin da yake biyan waɗanda suka ci kuɗin caca aka yi kuskuren aiko da ita gidan Thomas, shekara biyu bayan sun rabu.
Thomas ya yi matuƙar mamaki bayan ya gano cewa tsohuwar matarsa ta lashe har N1.5bn daga cacar jihar California sannan tana karɓar N25m a kowace shekara.
Nan da nan Thomas ya kai ta ƙara gaban kotu bisa saɓawa dokar bayyana kadarori ta jihar da yin zamba cikin aminci da mugunta.
Wata kotun ma'aurata a Los Angeles ta yarda koken da Thomas ya kai inda ta ba shi dukkanin kuɗin da Denise ta lashe a caca.
"Ba Zan Amsa Ba Sai Kin Duƙa Kan Guiwa" Bidiyon Yadda Wani Magidanci Ya Ƙi Karban Abinci Daga Matarsa Ya Ja Hankali
Alƙalin ya ce da Denise ta fayyace gaskiya da ta samu rabin kuɗin, amma ta rasa wannan damar tun da ta ɓoye gaskiya.
Ango Ya Nemi Saki a Kotu Kwana 2 Bayan Daurin Aure
A wani labarin kuma wani sabon ango ya garzaya kotu neman a raba auren da ke tsakaninsa da amaryarsa kwana biyu bayan an ɗaura musu aure.
Angon dai ya harzuƙa ne bayan amaryar tasa ta rama marin da mahaifiyarsa ta yi mata lokacin da rigima ta kaure a tsakaninsu.
Asali: Legit.ng