"Ku Daure Ku Dawo": Lakcara Dan Najeriya Ya Roki Dalibansa Da Su Daure Su Dawo Makaranta
- Wani lakcara ɗan Najeriya, ya nuna halin kirki inda ya aike da wani roƙo ga ɗalibansa waɗanda ba su dawo makaranta ba
- Yayin da yake yin wani bidiyo a cikin aji wanda ba mutane sosai a ciki, lakcaran ya buƙace su da su yi ƙoƙarin dawo wa makaranta
- A cewarsa hukumomin makarantar sun umarci da a fara karatu da wuri ba tare da wani ɓata lokaci ba
Bidiyon wani lakcara ɗan Najeriya ya bayyana inda yake roƙon dalibansa da su daure su dawo makaranta.
Bidiyon da ya ɗauka a cikin aji, akwai ƴan tsirarun ɗalibai a ciki inda ya yi roƙon nasa cikin tausasa murya.
Ya bayyana cewa an ci gaba da karatu kuma hakan ya biyo bayan umarnin da hukumomin makarantar suka bayar ne.
Lakcaran da farko ya fara da gargaɗi ne amma daga baya sai ya koma yana ba ɗaliban baki da kada matsalar rashin isassun kuɗaɗe ta karya musu gwiwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Lakcaran ya buƙaci su daure su dawo makaranta
Ya ƙarƙare roƙon nasa da yin addu'a inda ya nanata cewa ɗaliban su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun dawo makaranta.
A kalamansa:
"Yanzu da mu ka fara karatu, ku da ku ke a gida, idan kun ga dama ku dawo, idan kun ga dama kuma kada ku dawo."
"Hukumar makaranta ta umarce mu da mu fara karatu. Tuni mu ka fara tattaunawa. Karatu ya kankama."
"Abinda ya fi dace mu ku shi ne, ku daure ku dawo makaranta da ɗan abinda ku ke da shi. Ku daure kawai ku dawo makaranta. Mun san cewa abubuwa sun yi tsauri. Ku gayawa baba da mama ko da N1, N10, su daure su ba ku ta yadda za ku dawo makaranta."
"Allah zai kawo mafita. Ku daure kawai ku dawo."
Matashi Ya Bar Aikinsa Saboda Budurwa
A wani labarin, wani matashi ya koka bayan ya aikata wani kuskure wanda ya sanya shi ya dawo yana cizon yatsa.
Matashin ya bayyana cewa ya ajiye aikinsa saboda yana son kasancewa da budurwarsa wacce ba su zaune a gari ɗaya.
Sai dai, bai daɗe da komawa wajen na ta ba budurwar da ya ajiye aikin saboda ita ta rabu da shi gaba ɗaya.
Asali: Legit.ng