“Na Tsani Cacar Wasanni”: Yaro Ɗan Shekara 19 Ya Ci N38m Da N450, Mahaifinsa Ya Ce Ya Mayar Da Kuɗin
- Wani yaro ɗan shekara 19 ya ci N38m a cacar wasanni da ya buga, amma mahaifinsa bai ji daɗin hakan ba, ya nemi ya mayar da kuɗin
- An ce yaron ya sanya N450 kacal, a yayin da kuma ya ciyo maƙudan kuɗaɗe, sai dai mahaifinsa ya ce caca ba abu ba ce mai kyau
- A labarin wanda ya yi fice, ɗan uwan yaron ya aiko da saƙo ba tare da sa sunansa ba, yana neman shawarar yadda za su shawo kan mahaifinsu
Wani mutumi ya nemi ɗansa ya mayar da Naira miliyan (N38m) da ya ciyo ta hanyar buga cacar wasanni.
Yaron wanda aka ce yana da shekaru 19 a duniya, ya sanya N450 kacal, inda ya ciyo N38m sannan ya zo da kuɗin gida.
Caca ba abu ba ce mai kyau
Mahaifinsa, ya bayyana cewa yin fare ko kuma cacar wasanni a matsayin wani abu ne mara kyau, kuma nan take ya nemi yaron da ya mayar da kuɗin zuwa inda suka fito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Labarin dai na ƙunshe ne a cikin wani saƙo da ba a bayyana sunan wanda ya turosa ba da aka aika ta dandalin aika saƙon nan NGL.
Cikakken saƙon ya bayyana daga baya a yanar gizo, haka nan, shafin CorrectNG ma ya wallafa shi.
Yaron ya nemi jin ta bakin al'umma
A cikin saƙon, dan uwan yaron yana neman shawara wurin al'umma kan yadda za su shawo kan lamarin.
Ya koka kan cewa yanzu haka kuɗin hayar su ya ƙare duk da haka mahaifin na su ya ƙi amincewa da kuɗin, wanda hakan har saɓani ya haifar tsakaninsa da mahaifiyarsu.
Ya ƙara da cewa mahaifin ya ƙeƙashe ƙasa ya ce a mayar da kuɗin duk da an nuna masa katin buga cacar.
Yadda aka yi da mahaifin
Ga saƙon kamar yadda aka wallafa shi:
“Ƙani na ɗan shekara 19 ya ci N38m da N450, amma mahaifinmu ya fututtuke cewa ya mayar da kuɗin, saboda bai yarda da yin caca ba, duk da an nuna masa tikiti, har yanzu ya ƙi yarda.
"Nan da wata biyu kuɗin hayarmu zai ƙare, hakan ya janyo matsala tsakaninsa da mahaifiyarmu. Ina neman shawara."
Matashi ya yi wa mahaifiyarsa gagarumar kyauta
A wani labarin da muka wallafa a baya, wani matashi ya gwangwaje mahaifiyarsa da gagarumar kyauta a ranar da ta ke murnar zagayowar ranar haihuwarta.
Yaron dai ya cikawa mahaifiyar ta sa burinta da ta daɗe ta na son ganin cikarsa na yin tafiya a jirgin sama.
Asali: Legit.ng