Ba Na Bukatar ‘Gas’: Budurwa Ta Yi Amfani da Zafin Rana Wurin Soya Kwai Guda 2 a Dubai

Ba Na Bukatar ‘Gas’: Budurwa Ta Yi Amfani da Zafin Rana Wurin Soya Kwai Guda 2 a Dubai

  • A wani faifan bidiyo da ya yadu a kafar sada zumunta, an gano wata budurwa ta na soya kwai da zafin rana a Dubai
  • Budurwar ta ce zafin rana kadai ya watadar idan mutum yana son soya kwai, ta soya kwai din ba tare da tukunyar gas ba
  • An gano budurwar ta dauko kwalbar man gyada ta zuba a cikin kwanon suya, daga bisani ta fasa kwai a ciki ta fara soyawa

Wata budurwa da take rayuwa a Dubai ta bai wa mutane mamaki lokacin da ta soya kwai da zafin rana.

Budurwar ta ce ta yi nasarar soya kwan ne ba tare da amfani da wani abin yin girki ba, ta ce zafin rana kadai ya wadatar.

Budurwar ta soya kwai da zafin rana
Budurwar Lokacin da Take Amfani da Zafin Rana Wurin Soya Kwai a Dubai. Hoto: TikTok/@mercy_gains1.
Asali: TikTok

A wani faifan bidiyo wanda @mercy_gains1 ta wallafa, an gano budurwar ta dauko abin suya ta ajiye shi a rana.

Kara karanta wannan

Bangarori 7 da Ake Jiran Bola Tinubu Ya Kawo Gyara Idan Ya Gaji Muhammadu Buhari

Budurwa ta soya kwai da hasken rana

Sannan ta dauko kwalbar man gyada ta zuba mai a cikin kwanon suya, daga bisani ta fasa kwai guda biyu a ciki ya fara soyuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da farko budurwar babu takalmi a kafarta amma daga baya dole ta dauko takalmi saboda tsananin zafin rana.

Mutane sun sha mamaki

Faifan bidiyon ya bai wa mutane da dama mamaki, wasu daga cikinsu suka ce daman abin suyar da zafinsa kafin ta dauko shi.

Yayin da wasu mutane suke kokwanton cewa babu yadda za a yi mutum ya soya kwai da zafin rana kadai.

Kalli faifan bidiyon a kasa:

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu:

@Joanna:

“Wa ya fahimci cewa abin suyan daga kan wuta aka dauko shi.”

@Habib Beye:

“Amma kuma har takalminta ta cire.”

@user2001509101289:

Kara karanta wannan

"Sai Wasa Da Maza a Jeji": Mahaifiya Ta Fallasa Sakamakon 'Yarta Budurwa, Kalaman Malamarsu Ya Jawo Muhawara

“Ina fada maka, har kuka na yi lokacin da na ke tafiya wurin aiki.”

@loverboy:

“Wadanda ke Dubai kadai za su fahimta.”

@E & V:

“Abin suyan daman ya riga ya yi zafi, kin ce zafin rana amma kuma ba ki saka ko takalmi ba.”

Mutane Da Dama Sun Yabi Kyakkyawar Budurwar Da Ta Dukufa Neman Na Kanta

A wani labarin, wata budurwa 'yar Najeriya ta wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna yadda ta ke neman na kanta.

An sarrafa wurin kasuwancin da katakai da kuma tukunyar gas da abin gwaji don siyar da gas ga mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.