"Sai Wasa Da Maza a Jeji": Mahaifiya Ta Fallasa Sakamakon 'Yarta Budurwa, Kalaman Malamarsu Ya Jawo Muhawara
- Sakamakon wata budurwa 'ya yi muni, ta faɗi duka darusan da aka musu a makaranta, ya jawo muhawara a Intanet
- Malamarsu a nata jawabin, ta shawarci budurwar da ta bar makarantar ta je ta yi aure tunda ta kasa cin jarrabawa
- Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi muhawara game da hoton sakamakon, da yawa daga ciki sun zargi budurwar da rashin mayar da hankali kan karatun ta
Wata budurwa ta yamutsa kafar sada zumunta ta da yanar gizo bayan yaɗa hoton sakamakon jarabawarta da aka yi.
Budurwar dai ta gaza cin darussan da ake koyawa ma ta a makaranta, hakan ya sanya malamar da ke koyar da ita yin bayani kan abinda ya jawo ma ta faɗuwar.
A cewar malamar, yarinyar ta kasance ta na sha'awar yin wasa da maza a ko da yaushe cikin daji da ke kusa da makarantar.
Rashin Aiki Ko Kwakwaf: ’Yar Najeriya Ta Bude Buhun Shinkafa, Ta Fara Kirge Don Sanin Kwaya Nawa Ne a Ciki
Ganin haka ne ma ya sa ta shawarci budurwar da kawai ta yi aure ta manta da batun karatu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Koyaushe sai wasa tare da yara maza a cikin daji. Ba ta iya taɓuka komai cikin kowane nau'in wasannin makaranta. Ina ba ta shawarar tayi aure, "
An dora hoton sakamakon ne a shafin Instagram na @mediagist
Ra'ayoyin jama'a a kafafen sada zumunta
@jacob Nwose ya ce:
"Lallai ta na da buƙatar ɗaukar shawarar da mahimmanci. Ta ya ya yaro zai faɗi duka darussa?"
Matthias Ugwu cewa ya yi:
"Ɗaya daga cikin dalilan da yasa nake tsoron samun ɗiya mace a wannan zamani kenan, yara mata sun fi samun matsala, da wuya ne ka samu ta gari a zamanin nan."
Deremi_ ya ce:
"Domin Allah ta na bukatar yin auren."
@Dennis Okwukwe kuma ya ce:
"Kullum wasa da samari a daji? Ke me kika yi a matsayinki na malama?"
Pascal James ya ce:
"Daga ranar da ɗiya ta ta zo min da irin wannan sakamakon, to fa ta bar makarantar kenan."
Ga hoton daga shafin Media Gist
Wata Yarinya ta ɗora takardar jarabawar ta a Intanet
A wani labarin na daban kuma, Legit.ng ta kawo muku rahoton wata yarinya da ta ɗora hoton takardar jarabawar ta da ya rikita yanar gizo.
An ba ta takardar ta da aka gyara ta jarabawar da suka yi, amma cikin kaɗuwa sai ta ga ba ta ci komai ba.
Asali: Legit.ng