"Da Na Kowa Ne": Uwa Ta Fadi Yadda Lakcara Ya Kore Ta a Aji Don Kukan Jinjiranta, Bidiyon Ya Janyo Cece-Kuce
- Wata mata ta wallafa wani faifan bidiyo inda ta ke bayyana yadda malami ya koreta a cikin aji da ‘yarta
- Malimin ya kore ta ne saboda ‘yarta ta yi kuka wadda hakan ya fusata matar da cewa ya ci mutuncinta
- Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu yayin da kusan dukkansu suke ganin malamin bai kyauta ba
Wata mata a Najeriya ta bayyana yadda wani malaminsu ya fatattaketa a aji saboda kukan jaririyarta.
Matar mai suna @sheisteemah a wani faifan bidiyo a TikTok ta halarci aji don daukar darasi a makarantar tare da ‘yarta karama wadda ko tafiya ba ta iya ba.
A lokacin da malamin ke koyarwa, sai ‘yar ta kwarara ihu wanda hakan ya fusata lakcaran nasu inda shi kuma bai yi wata-wata ba dukkansu ya kore su daga ajin.
Matar ta nuna bacin ranta yadda malamin ya ci mutuncincu a cikin bidiyon, amma sai ta ce ba laifinsa ba ne laifin yarinyar ne ita ta jawo mata cin mutunci.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Matar ta yi rubutu kamar haka:
“Yar ka za ta jawo maka cin mutunci saboda yin kuka a aji, malamin kuma ya kora mu waje gaba daya”.
Ga bidiyon a kasa:
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu
@omolara233:
“Karki damu. ‘Yarki za ta kawo miki alkairai.”
@slimzzy826:
“Malamin ba shi da yara ko, watakila ‘yar ta tsane shi.”
@mokebaby:
“Haka su ke yi kaman ba su da yara a gida, ‘yar ki alkairi ce.”
hunsuestheryemayi:
“Kar ki damu haka suke kaman ba su haifi ‘ya’ya ba, yaran su na gida tare da mamansu ita kadai.”
@leachiey:
“Hhhhh don Allah ki yafe mata. Yanda ba ta son kallon abin daukar hoton kaman ta san laifin da ta yi.”
"Soyayyar Nesa Akwai Wuya": Matashi Ya Sharbi Kuka Yayin Da Kyakkyawar Budurwarsa Baturiya Zata Koma Kasarsu
@pweetyej:
“Wani malaminmu duk lokacin da wani jariri ke kuka, zai dauke shi kafin wani lokaci jaririn ya yi bacci.”
estherlovth:
“Me ya sa kuke yi masa kallon bai kyauta ba, kukan wasu yaran ya na dauke hankalin malamin da kuma dalibai.”
UwaTa Ɗaure Ƙafar Ɗanta a Kujera Saboda Ɓarnar Da Yake Yi Mata a Shago
A wani labarin, wata uwa ta daure kafar danta a jikin kujerar shago saboda tsananin rikicin yaron, wanda kullum sai ya jawo mata asara.
A cikin wani faifan bidiyo, an gano matan cikin fushi tana nuna yadda ke mata barna, da kuma yadda ya yi kaca-kaca da shagon cikin kankanin lokaci.
Asali: Legit.ng