“Maganin Yara Maras Ji”: Bidiyon Yadda Mata Ta Ga Ana Siyar Da Bulala A Turai Ya Ba Da Mamaki

“Maganin Yara Maras Ji”: Bidiyon Yadda Mata Ta Ga Ana Siyar Da Bulala A Turai Ya Ba Da Mamaki

  • Wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafar sada zumunta an gano wani shago makare da bulali a kasar Amurka
  • Matar da ta wallafa faifan bidiyon ta ce tayi matukar mamaki tarin bulalin a shago har siyar da su ake yi a kasa irin Amurka
  • Shagon da ake siyar da bulalin dai na wasu `yan Nahiyar Afirka ne da ke rayuwa a kasarta Amurka

Wata `yar Najeriya da ke rayuwa a kasar Amurka ta ga abun mamaki lokacin da shiga wani shago ta ga tarun bulali.

Bulala dai wani abu ne da iyaye kan siya su ajiye kuma suke amfani da shi wurin hukunta yara in sun aikata ba dai dai ba.

Bidiyon wata mata ya yadu a kafar sada zumunta in da ake siyar da bulali a Amurka
Lokacin da matar ta ke nuna bulalin, Hoto: TikTok
Asali: TikTok

Matar wadda ta ke rayuwarta a kasar Amurka, tayi mamakin yadda ta ga bulala ana siyar da shi a kasar abun da bata yi tsammani ba, ta dauki faifan bidiyo bulalar ta kuma yada shi a kafar sada zumunta.

Kara karanta wannan

Kamar danki: Bidiyon wada lokacin da matarsa ke shafa masa ya jawo cece-kuce

Shagon na su waye

Amma ta tabbatar da cewa shagon da ta samu tarun bulalin mallakin `yan Afrika ne a Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shagon ya tabbatar mata cewa lokacin da tazo ta samu bulalin ma sun kare, don kullum jakar a cike ta ke fal da bulali, hakan ya nuna yawan siyan bulalin da ake yi a shagon.

Matar ta ja hankalin mutane da su hukunta `ya`yansu amma kar su bi irin tsarin Amurkawa in da ba`a hukunta yara.

Faifan bidiyon ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta zamani, inda mutane da dama suka tofa albarkacin bakinsu bayan ganin bidiyon da @hildaehidiamen ta yada.

Kalli bidiyon:

Martanin wasu mutane a dandalin sada zumunta

@Hamond Yvese:

“Wannan shi ne masarrafar Afirka”

@Ademola:

“Ina tuna lokacin da iyaye na ke bamu kudi mu siyo bulala kalar zabinmu, hhh. Kai nayi kewar kasancewata yaro”

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tasa Keyar Jami'in Bogi Na EFCC Zuwa Gidan Gyaran Hali

@coolme464:

“Wannan shi ne abu mafi kyau da Amurka ta ke bukata, ya na kore shiririta cikin minti daya”

@Julie:

“A kasar Uganda muna kiranta kyiboko. Kuma ba ta da wani doka wurin amfani, ko ta yaya, Allah ya taimaki iyayenmu a dalilin haka ba za`a dake mu yanda ake so ba.

@universal:

“Ina bukatan daya ga `da na”

Likita Ya Yi Gargadi Kan Amfani Da Tukwanan Zamani na ‘Non-stick’, Bidiyon Ya Yadu

A wani labarin, Likitan Najeriya, Chinonso Egemba ya gargadi mutane a kan amfani da tukwanan 'non-stick' da cikinsu suka babbare.

A cewar likitan, an lullube tukwanan 'non-stick' da sinadaran Polyfluoroalkyl substances (PFAS), wadanda bai kamata ace sun bare ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.