Yin Koyi Da Yesu: Fasto Ya Mutu Yana Tsaka Da Azumin Kwana 40

Yin Koyi Da Yesu: Fasto Ya Mutu Yana Tsaka Da Azumin Kwana 40

  • Wani fasto yace ga garin ku nan bayan yayi ƙoƙarin yin koyi da abinda Yesu Almasihu yayi a cikin bible
  • Faston yayi ƙoƙarin yin koyi da azumin kwana 40 wanda Yesu Almasihu yayi a lokacin rayuwar sa
  • Bayan ƴan'uwan sa sun lura da yana shirin mutuwa sun garzaya da shi asibiti inda daga baya yace ga garin ku nan

Wani fasto ɗan ƙasar Mozambique ya rigamu gidan gaskiya bayan ya shafe kwana arba'in yana azumi, a ƙoƙarin sa na yin koyi da abinda Yesu Almasihu yayi a cikin littafi mai tsarki na addinin kirista.

An tabbatar da mutuwar faston mai suna Francisco Barajah, wanda shine ya kafa cocin Santa Trindade Evangelical, a tsakiyar gundumar Manica, a ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairun 2023. Rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

Aisha Ta Goyi Bayan Shawaran Da Tinubu Ya Bada Kan Sabbin Kuɗi, Tayi adawa da na Shugaba Buhari

Church
Yin Koyi Da Yesu: Fasto Ya Mutu Yana Tsaka Da Azumin Kwana 40
Asali: UGC

Ya mutu yayin da ake duba lafiyar sa a wani asibiti a Beira, inda aka ɗauke shi cikin wani mawuyacin hali.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan yayi azumin kwana 25, nauyin sa yayi matuƙar raguwa wanda har ta kai baya iya tashi, wanka ko tafiya. Lamarin ya ƙara ta'azzara bayan da aka kai kwana na 38.

Kwanaki kaɗan bayan hakan, ƴan'uwan sa da mabiya cocin sa, sun matsa lamba inda aka kai shi asibiti, amma ba a samu nasarar samo lafiyar sa ba.

Duk da ƙoƙarin da ma'aikatan lafiya na asibitin suka yi domin ganin ya samu lafiya, lamarin ya faskara inda daga ƙarshe yayi bankwana da duniya.

Mabiya a cocin sa da makabtan sa sun cika da mamakin yadda abubuwa suka kaya, saboda yadda ya rame matuƙa ya fita cikin hayyacin sa a cikin ƴan kwanakin da yayi yana azumin.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamna Wike Ya Yi Magana Ta Karshe Kan Yuwuwar Sulhu da Atiku Ana Dab da Zaɓen 2023

Hisbah ta Damke Malamin Islamiyya, Ana Zargin Shi da Laifin Lalata da ‘Dalibansa

A wani labarin na daban kuma, wani malamin makarantar Islamiyya ya shiga hannun hukuma, bisa zargin sa da ɗaliban da yake koyarwa.

Tuni dai hukumar Hisbah ta fara bincike kan malamin makarantar wanda ya aikata wannan ɗanyen aikin a makarantar da yake koyarwa ta mahaifin sa, wanda yanzu ya rigamu gidan gaskiya.

Lamarin dai ya auku ne a unguwar Nasarawa, cikin ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida