Bincike ya nuna dukiyar Attajirai 2 za ta iya fito da mutum miliyan 63 daga talauci

Bincike ya nuna dukiyar Attajirai 2 za ta iya fito da mutum miliyan 63 daga talauci

  • Ana lissafin Aliko Dangote da Mike Adenuga sun mallaki dukiyar da ta kai fam Dala biliyan 20 a yau
  • Maganar da ake yi a yanzu, arzikin Shugaban kamfanin BUA ya kai $4.8bn (Naira tiriliyan biyu)
  • Binciken da aka yi, ya nuna dukiyar wadannan mutane ta zarce na mutane miliyan 63 a Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Nigeria - Idan aka hada dukiyar Alhaji Aliko Dangote da na Mike Adenuga, su biyun kawai sun fi mutane miliyan 63 da ke Najeriya yawan arzikin kudi.

Wani rahoto da ya fito daga Oxfam, ya nuna Attajiran da ake ji da su, sun fi daya bisa ukun ‘yan Najeriya arziki, idan za a tattara duk abin da suka tara.

Aliko Dangote shi ne shugaban kamfanin Dangote Group, Mike Adenuga ne wanda ya mallaki kamfanin sadarwa na Globacom da ya yi fice a Najeriya.

Kara karanta wannan

Mawakin Duniya zai yi zaman kurkukun shekara 30 saboda lalata da ‘yan mata da yara

Rahoton ya tabbatar da cewa dukiyar manyan Attajiran kasar nan ta karu sosai a lokacin annobar COVID-19, sa’ilin da sauran jama’a suka kara tsiyacewa.

Taron WEF na 2022

Oxfam ya gabatar da wannan rahoto da ya nuna irin tazarar da ake samu tsakanin masu hali da marasa shi a Najeriya domin shiryawa taron WEF da za ayi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Henry Ushie ya yi wannan karin haske ne kafin babban taron da za a yi a kasar Switzerland.

Aliko Dangote
Mai kudin Afrika, Aliko Dangote
Asali: UGC

Mutane 3 sun fi mutum miliyan 60

Attajirai uku da suka fi kowa kudi a kasar nan sun mallaki Dala biliyan 24.9 Sai an hada talakawa fiye da miliyan 60 sannan za a iya fito da wannan dukiya.

Baya ga Dangote da Adenuga, na uku a jerin shi ne Rabiu Abdulsamad mai kamfanin nan na BUA.

Kara karanta wannan

Tallafin fetur: Majalisa za ta binciki Gwamnatin Buhari, ta ce an sace Naira Tiriliyan 2.9

Alhaji Rabiu Abdulsamad ya na da fiye da Dala biliyan 4.8 a yau. Kwanakin baya har an fitar da rahoto cewa Attajirin ya sha gaban Adenuga a na biyu.

A lissafin da aka yi, Aliko Dangote yana da kusan Dala biliyan 14 (N5tr kenan a kudin Najeriya a yau). Sannan Adenuga ya na da Dala biliyan 6.5 (N2.7tr)

Binciken da TheWhistler ta yi ya nuna 38% ya karu a dukiyar wadannan masu kudi, a sa’ilin da mutane sama da miliyan 7 suka sake burmawa tarkon talauci.

Inda matslar ta ke a Najeriya - Masani

Mun yi hira da Tijjani Ahmed wanda masani ne a harkar tattalin arziki, wanda ya yi mana karin haske a kan abin da ya jawo karin tazara tsakanin bangarorin.

Tijjani Ahmed ya ce daga cikin abin da ke jawo matsala shi ne dukiyar kasa ta tattaru a hannun tsirarun mutane wanda suke juya ta, yayin da saura ke wahala.

Kara karanta wannan

A cikin awanni 8 rak, Elon Musk ya tara abin da Aliko Dangote ya mallaka gaba da baya

A bangaren tattalin arziki, Ahmed ya ce darajar kudi ta ragu sosai, don haka tattalin arziki ya rugurguje. Baya ga haka, akwai matsalar tsare-tsaren gwamnati.

Laifin ba a kan gwamnati kadai yake ba, masanin ya ce a Najeriya ana samun matsalar yawon dogaro a kan wani mutum daya musamman a gidajen talakawa.

Su kuwa masu kudi ba su cika tara iyali ba, sannan matansu su na neman na kansu. Har ila yau, talaka bai samun isasshen ilmin da zai sa ya samu aiki mai tsoka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng