Tsaleliyar Budurwa Za Ta Auri Direban Napep Da Ta Ba Wa Lambar Wayarta Shekaru 5 Da Suke Shuɗe

Tsaleliyar Budurwa Za Ta Auri Direban Napep Da Ta Ba Wa Lambar Wayarta Shekaru 5 Da Suke Shuɗe

  • Ana ta yi wa wata ‘yar Najeriya sambarka bayan ta bayyana batun sanya ranar aurenta da masoyinta
  • A cewarta, ta yarda da batun aurensa bayan shekaru 5 da saurayin, wanda direban Napep ya amshi lambar wayarta
  • Yayin da ta wallafa kyawawan hotunan sa ranar ta su, ta bayyana cewa labarin soyayyarsu mai tsawo ne

Wata ‘yar Najeriya mai suna Lydiv Ogbansiegbe ta bayyana cewa akwai wata natsuwa ta musamman da ke samun mutum idan ya hadu da wanda ya ke so.

Lydiv ta wallafa hotunan sa ranar aurensu a shafinta na Instagram wanda su ka kayata shagalin sosai.

Kyakkyawar Budurwa Za Ta Auri Direban Keke Napep Bayan Shekaru 5 Bayan Bashi Lambar Wayarta
Budurwa Za Ta Auri Direban Keke Napep Bayan Shekaru 5 Bayan Bashi Lambar Wayarta. Hoto: Photo Credit: @miss_lydiv
Asali: Instagram

Yadda Lydiv ta hadu da mai keke Napep din

A cewar kyakkyawar budurwar, sun hadu ne yayin da ta hau Keke Napep.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

2023: APC ko PDP duk wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa zan taya shi murna, Hadimar Buhari

Lydiv ta ce shekaru 5 kenan da ta ba shi lambar wayarta, sai ga shi yau ya zo neman aurenta.

Kamar yadda ta wallafa:

“Akwai wani kwanciyar hankalin da ke riskar ka idan wanda ya dace da kai ya zo gare ka.
“Shekaru biyar da su ka shude na bai wa wani direban Keke Napep din lambar wayata.
“Jiya da dare na amince da tayin aurensa. Labari ne mai tsawo dangane wannan soyayyar.
“Ina matukar son ka nawa.”

‘Yan Najeriya sun yi ta tsokaci karkashin wallafar

comedian_aboki44 ya ce:

“Kai ina taya su murna. Soyayya abu ce mai kyau idan ka hadu da wanda ku ka dace.”

theunlimitedmusic ya ce:

“Ban gane wannan labarin ba, amma ina taya ku murna... Na fara tunanin siyan Keke fa... Kila in hadu da masoyiyata ta asali. Na manta, idan aka hada da mutum ku abin ya fi aiki.”

Kara karanta wannan

Ke duniya: 'Yan sanda sun damke magidanci da ya tura matarsa karuwanci, ya siyar da 'dan shi

official_soicm ya ce:

“Kawai mutum ya fara sana’ar Keke ne. Don Allah wa ke da keke wacce zan dinga ba shi kudi karshen ko wanne mako?”

omogealagbo1 ta ce:

“Ba zan bayar ba. Idan mai keke ya amshi lambar wayarki a Ibadan sai kin mutu saboda yawan kira, za ki yi ta shan jar miya dai.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: