Abin da ya dace da ‘Yan Majalisar Tarayya a kan bacewar Dadiyata inji Sanata Shehu Sani

Abin da ya dace da ‘Yan Majalisar Tarayya a kan bacewar Dadiyata inji Sanata Shehu Sani

  • Kwamred Shehu Sani ya tofa albarkacin bakinsa a kan mutuwar mahaifiyar Abubakar Dadiyata
  • Tsohon Sanatan jihar Kaduna ta tsakiya ya yi addu’a ga Ubangiji Ya jikan wannan Baiwar Allah
  • Shehu Sani ya bukaci ‘Yan majalisar tarayya su kawo maganar matashin da aka dauke tun a 2019

Kaduna - Shehu Sani wanda ya taba wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, ya yi magana game da mutuwar tsohuwar Abubakar ‘Dadiyata.’

A makon da ya wuce mahaifiyar wannan matashi, Abubakar Idris (wanda aka fi sani da Dadiyata) wanda ya yi suna wajen sukar gwamnati ta bar Duniya.

Sanata Shehu Sani ya koka a kan yadda wannan Baiwar Allah ta rasu ba tare da burinta ya cika ba. Har ta rasu, ta na begen ganin yaronta da aka dauke.

Babban ‘dan siyasar ya yi addu’a ga Ubangiji ya jikan wannan mata da ta riga mu gidan gaskiya, kuma ya bukaci tsofaffin abokan aikinsa su yi hobbasa.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike: Da Zarar 'Yan Ta'adda Sun Ji Sunana Za Su Tsere

A ranar Laraba, 20 ga watan Afrilu 2022, Sanata Shehu Sani ya yi wannan magana a shafin Twitter.

Abin da Shehu Sani ya fada

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mahaifiyar Dadiyata ta rasu ba tare da ganin dawowar ‘danta da ta ke kauna da aka dauke ba.”
Uwar Dadiyata
Mahaifiyar Dadiyata Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Allah Ya jikanta da gafara. Ya kamata ‘yan majalisar tarayya na Kaduna su cire tsoro, su jajirce wajen tsayawa Dadiya a zauren majalisa.”
“Su yi magana a game da halin da ‘yan uwansa su ke ciki. Shirunsu abin kunya ne.”

- Shehu Sani

Shirun ‘yan majalisa

Legit.ng Hausa ba ta da labarin cewa akwai wani ‘dan majalisar tarayya mai wakiltar jihar Kaduna da ya taba kawo wannan batun a gaban majalisar Najeriya.

Daiyata ya tashi ne a cikin garin Kaduna, an kuma dauke shi ne a gidansa da ke unguwar Barnawa. amma asalinsa mutumin garin Madobi ne da ke jihar Kano ne.

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

Shekaru uku babu labari

Shekaru kusan uku da suka wuce wasu mutane da ba a sansu ba, suka yi awon gaba da Dadiyata a gidansa da ke garin Kaduna, har yau babu wani labarinsa.

Wannan ya tada hankalin iyaye, ‘yanuwa da masoyan wannan Bawan Allah. Babu shakka mahaifiyarsa, Fatima Idris za ta fi kowa shiga cikin damuwa.

Daga cikin ‘ya ‘yanta akwai Abubakar (Dadiyata), Usman (Malam), Aliyu da kuma Aminu.

"Lafin jami'an tsaro ne"

A can kwanakin baya aka ji Aminu Abdussalam Gwarzo, daya daga cikin jagororin Kwankwasiyya a Najeriya yana kokawa game da batar ‘Dadiyata’.

Gwarzo ya ce nauyin gano Dadiyata ya rataya kan jami'an tsaro. Amma DSS sun tabbatar da cewa ba ya hannunsu. ‘Yan Sanda kuma sun ce su na bakin kokarinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel