Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Girgiza Yan Najeriya

Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Girgiza Yan Najeriya

  • Masu amfani da kafafen sada zumunta sun maida martani kan wasu hotunan kafin Aure na yar Najeriya da ya watsu
  • Ba tantama hakan na da alaƙa da gajartar mutumin idan aka kwatanta da girman jikin kyakkyawar budurwan
  • Yan Najeriya da dama sun bayyana cewa Ma'auratan kyakkyawan misali ne na soyayyar gaskiya da ta yi ƙaranci

Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya ta tashi daga bangaren yan mata yayin da ta shirya amarcewa da Masoyinta, wanda surar jikinsa ta nuna gajere ne.

Hotunan kafin aure na ma'auratan da Amaryan ta watsa a kafafem sada zumunta, shafin Gossipmilltv ya sake tura su a kafar sada zumunta ta Instagram.

Hotunan Kafin Aure.
Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Girgiza Yan Najeriya Hoto: @gossipmilltv
Asali: Instagram

Sanye da karamar riga iri ɗaya da wando Jeans, tsintsayen soyayyar biyu sun nuna tsantsar soyayya a Hotunansu na Kafin Aure da murmushi a fuskarsu.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet

A wani Hoton kuma masoyan biyu sun fito a cikin kayan Atamfa, yayin da suka rungumi juna kuma suka kalli Camarar dake ɗaukar su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har zuwa san da muka haɗa wannan rahoton, babu taƙamaiman ranar ɗaura Auren masoyan.

Martanin yan Najeriya

@foodium.co ta ce:

"Ya Allah, bani da matsala da rashin tsayinsa saboda nima gajera ce, amma Dan Allah ka sa ya zama kyakkyawa ko kaɗan ne."

@foodium.co ya ce:

"Wasu daga cikin su zasu fara zuwa suna izgili kan wannan abun, ba wani abun damuwa bane a wurin su."

@abayaehi_ ya ce:

"Duk wanda ya samu soyayyar gaskiya ya samu abu mai kyau. Murnar rayuwar aure gare su. Allah ya yi wa auren su Albarka Ameen."

@bakareyetty ta ce:

"Mun haɗuwa da soyayyar gaskiya a wurin da bamu tsammani, Allah ya musu Albarka, wannan itace soyayya ta gaskiya."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun kutsa har cikin gida sun kashe wani fitaccen Attajiri a Katsina da Azumi

A wani labarin kuma Gwamna Yahaya Bello dake neman takarar shugaban ƙasa ya ce ya maida aƙalla mutum 2,000 hamshaƙan masu kuɗi a jiharsa

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ce idan APC ta amince masa zai dauki mace ta farko ta zama mataimakiyar shugaban ƙasa a 2023.

Gwamna Bello ya ce gwamnatinsa ta canza rayuwar aƙalla mutum 2,000 zuwa hamshaƙan miliyoniya a Kogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262