Zuciyata ta daina ƙaunar mijina, Matar Aure ta nemi Kotun Musulunci ta raba auren
- Wata matar aure ta garzaya Kotun Musulunci a Kaduna ta nemi a raba aurenta saboda ba ta kaunar mijinta yanzu
- Matar ta kuma roki Kotun ta umarci mijinta ya barta ta kwashe karikitanta daga gidansa, zata biya kuɗin sadaki
- Sai dai a bangarensa mijin ya koka cewa da kuɗinsa ya siya mata kayan ɗakin, amma ya amince daga baya
Kaduna - Kotun Shari'ar Musulunci dake zamanta a Anguwar Magajin Gari, Kaduna, ranar Litinin, ta amince da bukatar wata matar Aure, Rakiya Ladan, na raba aurenta bisa hujjar ta dena kaunar mijinta.
Alƙalin Kotun Mai shari'a Nuhu Falalu, shi ne ya gimtse igiyoyin auren wanda ya shafe shekara 9, kamar yadda Jaridar Daily Trsut ta rahoto.
Alƙalin Kotun ya kuma umarci Magidancin mai suna Abba, ya bar matar ta zo ta kwashe karikitanta baki ɗaya daga cikin gidansa.
Mai Shari'a Falalu ya ce:
"Raba aure bisa bukatar mata yana cikin shari'ar addinin Musulunci amma bisa sharaɗin matar zata biya mijin kudin da ya biya na sadakinta."
"Allah ya albarkaci auren da samun ƴaƴa kuma wanda ake ƙara ba zai iya maida matarsa budurwa kamar yadda take kafin ya aureta ba."
Shin matar ta amince ta biya kuɗin sadakin da ya biya?
Tun da farko, Rakiya ta bakin Lauyanta, Abdulrauf Atiku, ta shaida wa Kotun cewa tana neman raba auren ne saboda babu sauran soyayyarsa a zuciyarta kuma ba zata iya zama a haka ba.
Ta faɗa wa alƙalin cewa a shirye take ta biya N20,000 da ya bayar a matsayin kudin sadaƙinta, dan haka ta roki Kotun ta umarci Magidancin ya barta ta kwahse kayanta daga gidansa.
Da yake martani, kafin ya amince ta kwashe kayanta, ya gaya wa Kotun cewa shi ya siya kayan da kuɗinsa.
A wani labarin kuma Uwar gida ta danna wa Mijinta wuka har lahira daga zuwa bankwana zai koma dakin Amarya
Tsagwaron kishin mata ya yi sanadin rasuwar wani Mai mata biyu yayin da yake yi wa Uwar gida bankwana zai koma dakin Amarya.
Rahoto ya nuna cewa Uwar gidan mai suna Atika ta daba wa mijinsu wuka har lahira a Mararaba dake jihar Nasarawa.
Asali: Legit.ng