Kasurgumin ɗan bindiga ya yi barazanar ɗaukar fansa kan mutane bayan Sojoji sun masa ɓarna
- Wani shugaban yan bindiga yan tura sakon barazana ga kauyuka a ƙaramar hukumar Kastina-Ala bayan soji sun kaddamar masa
- Rundunar sojin OPWS yayin da suka fita aikin tsaftace yanki daga ta'addanci sun tashi sansanin ɗan bindigan sun ƙashe wasu
- Shugaban ƙaramar hukumar, Alfred Atera, yace kasurgumin Terna Gide, ya faɗi matakin da zai ɗauka kan jama'a
Benue - Yan bindigan dake yankin ƙaramar hukumar Kastina-Ala a jihar Benuwai, sun yi barazanar kaddamar da harin ta'addanci kan ƙauyukan yankin.
Daily Trust ta rahoto yan ta'addan sun yi wannan barazanar ne biyo bayan sheƙe ƴan uwansu da dakarun sojin Operation Whirl Stroke (OPWS) suka yi.
Shugaban ƙaramar hukumar Kastina-Ala, Alfred Atera, wanda ya faɗi halin da ake ciki cikin damuwa, ya ce shugaban yan bindigan, wani Terna Gide, shi ne ya yi wannan barazanar ga ƙauyuka.
Dakarun sojin OPWS a ƙoƙarinsu na tsaftace yankin daga ayyukan ta'addanci ranar Talata, suka bindige yan bindiga hudu har lahira a wata musayar wuta.
Atera ya ce:
"Eh bayan harin da dakarun soji suka kai sansaninsu na Tse-Keji ranar Talata, suka tura yan bindiga hudu barzahu kuma suka tarwatsa sansanin, Terna Gide, ya yi wa ƙauyuka barazanar ɗaukar fansa."
"Da safiyar Laraban nan, ya kira waya yana barazanar cewa zai aikata ɗanyen aikin da ya zarce tarwatsa sansaninsa. Ya kira lambar ɗaya daga cikin yan Sa'kai dan yin barazana."
Yadda Sojoji suka tarwatsa sansanin yan bindiga
Wata majiya a rundunar soji ta bayyana cewa dakarun OPWS sun kaddamar da farmaki a yankin, kuma sun halaka yan ta'adda hudu.
"Ranar Talata dakarun mu dake zaune a Gbise ƙarkashin Kastina Ala sun fita tsaftace yanki kamar yadda suka saba, har suka ci karo da yan bindiga a Tse-Keji, an fafata a wurin amma sojiji suka ci karfin su."
"Yan bindigan suka tsere zuwa cikin jeji ba shiri kuma dauke da raunuka, amma sojoji sun musu ɓarna, hudu sun sheƙa barzahu nan take. Dakarun sun gudanar da bincike a wurin sannan suka ƙone sansanin."
A wani labarin kuma Jirgin yakin NAF ya yi luguden wuta a wurin shagalin auren kasurgumin ɗan bindiga, rayuka sun salwanta
Jirgin yaƙin rundunar sojin sama ya yi luguden wuta kan wurin shagalin bikin wani kasurgumin ɗan bindiga a Katsina.
Bayanai sun bayyana cewa luguden wutan ya yi wa yan ta'adda mummunan ɓarna, ya tura manyan su barzahu.
Asali: Legit.ng